Hukumar NDLEA Ta Kai Samame Legas da Ogun, Ta Lalata Haramtattun Kwayoyi da Dama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Lagos - Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta yi nasarar lalata haramtattun kwayoyi a jihohin Legas da Ogun.
Hukumar ta samu nasarar ne ranar Talata, 16 ga watan Afrilu.
A cikin sanarwar da hukumar ta fitar a shafinta na Facebook, ta tabbatar da lalata jimillar kilogiram 304,436 da kuma lita 40,042 na haramtattun kwayoyi da ta kama daga sassan jihohin Legas da Ogun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar ta lalata haramtattun kwayoyin ne da ta kama a bainar jama’a a Badagry da ke jihar Legas.
Shugaban hukumar na kasa, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya) ya ce lalata haramtattun kwayoyi da aka kama ya biyo bayan umarnin kotu ne.
Buba Marwa ya yi kira domin samun karin goyon bayan jama'a kan kokarin da hukumar NDLEA da sauran masu ruwa da tsaki ke ci gaba da yi na dakile matsalar shan da safarar miyagun kwayoyi a Najeriya.
Marwa ya kara da cewa kwayoyin da suka kama nau'o'i ne daban-daban da suka hada da koken heroin, kanabis da tramol.
Shugaban ya kuma mika godiyarsa ga sarakunan gargajiya, shugabannin hukumomin tsaro, malamai, kungiyoyi masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki da suka shaida lalata kwayoyin.
Yayin da yake tabbatar da cewa NDLEA ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarinta na kawo karshen matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a kasar, Marwa ya yi kira ga al'umma da su kara tallafawa ayyukan hukumar.
Gwamnan jihar Legas, Mista Babajide Sanwo-Olu wanda ya samu wakilcin shugaban karamar hukumar Badagry West, Mista Olusegun Onilude ya bayyana jin dadinsa da kokarin hukumar na shawo kan matsalar shan miyagun kwayoyi a kasar nan.
Ya kuma godewa hukumar kan yadda ta dauki wayar da jama'a a kan yaki da muggan kwayoyi zuwa makarantu da wurare mabanbanta a fadin jihar Legas.
A wani rahoton kuma, kun ji cewa hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta samu gagarumin nasara wajen yaki da ta'ammalli da miyagun kwayoyi a jihar Kano.
A cikin watanni 3, ta kama mutane 319 da ake zargi suna da hannu dumu-dumu cikin harkar kwaya a Kano, 14 mata sauran 305 kuma maza ne.
Asali: Legit.ng