Home Back

An Kai Harin Kunar Bakin Wake a Hanyar Kaduna Zuwa Abuja? Gaskiya Ta Bayyana

legit.ng 2024/10/5

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta yi watsi da rahotannin da ke cewa an kai harin ƙunar baƙin wake a hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Laraba.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya fitar.

Ba a kai harin kunar bakin wake a hanyar Kaduna zuwa Abuja ba
Gwamnatin Kaduna ta musanta kai harin kunar bakin wake a hanyar Kaduna zuwa Abuja Hoto: @ubasanius Asali: Twitter

Jaridar Tribune ta ce Samuel Aruwan ya raba sanarwar ne ga manema labarai ranar Laraba a Kaduna.

Kwamishinan ya bayyana cewa ko kaɗan babu ƙamshin gaskiya a rahotannin da aka yaɗa kan harin ƙunar baƙin waken.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Hankalin ma'aikatarmu ya kai kan rahotannin da ake ta yaɗawa, dangane da faruwar harin ƙunar baƙin wake ko makamancin haka a hanyar Kaduna zuwa Abuja."
"Ma'aikatar tana son ta fayyace cewa ya zuwa lokacin wannan sanarwar (ƙarfe 5:00 na yamma, Laraba 3 ga watan Yuli, 2024), babu wani abu makamancin harin ƙunar baƙin wake ko akasin haka da ya auku a hanyar Kaduna zuwa Abuja."
"Jami’an tsaro da majiyoyin leƙen asiri da ke kan hanyar suna gayawa gwamnati dukkanin halin da ake ciki.
"Rahotannin kai harin ba komai ba ne face kuskure zalla."
"Jami’an tsaron da aka girke a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja da ma yankin gaba ɗaya za su ci gaba da sanya ido domin tabbatar da tsaron ƴan ƙasa da matafiya."

- Samuel Aruwan

Asali: Legit.ng

People are also reading