Za a Iya Tsige Ganduje Daga Ofis Kamar Oshiomhole? APC Ta Yi Karin Haske
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sakataren yada labarai na jam'iyyar APC, Felix Morka ya yi magana kan turka-turkar da har yanzu ake yi kan batun tsige Abdullahi Ganduje daga shugaban jam'iyyar na kasa.
Morka ya shaida wa 'yan Najeriya cewa kuskure ne ayi tunanin halin da Ganduje yake ciki a yanzu iri daya ne da wanda Adams Oshiomhole ya shiga lokacin yana shugaban jam'iyyar.
Da wannan, sakataren yaɗa labaran ya ce jam'iyyar ba za ta iya tsige Ganduje daga kujerarsa ba kamar yadda ta tsige Oshiomhole a baya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Morka ya bayyana hakan ne a yayin zantawa da gidan talabijin na Arise a ranar Alhamis, lokacin da yake amsa tambayoyi kan batun tsige Ganduje daga shugaban jam'iyyar.
Idan ba a manta ba, a wani babban taro na jam'iyyar APC, kwamitin ayyuka na jam'iyyar ya tsige Oshiomhole daga kujerar shugaba, bayan ya riƙe muƙamin daga 2018 zuwa 2020.
Tsige Oshiomhole daga ofis alhalin yana da ragowar shekaru biyu a gaba ya jawo cece-kuce, inda tsohon shugaban jam'iyyar, Ntufam Eta ya ce an yi haka don a hana Bola Tinubu takarar shugaban kasa.
Amma a kan lamarin tsige Ganduje, Mr. Morka ya ce wadanda ke hanƙoron an kore shi ba halastattun 'ya'yan jam'iyyar bane.
"Shi Oshiomhole halastattun'ya'yan jam'iyyar ne suka taru suka tsige shi, amma Ganduje wasu bara-gurbi ne suka aikata hakan, kenan akwai banbanci a tsakaninsu.
"Muna so mu kara tabbatar wa duniya cewa wadanda suka fara kitsa batun tsige Ganduje daga jihar Kano ba mu sansu ba, basu da wani hurumi na tsige shugaban jam'iyyar."
- A cewar Morka.
Morka ya kuma ce har yanzu tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ne shugaban jam’iyyar APC na kasa.
Jaridar Vanguard ta rahoto Morka ya ce jam’iyyar ba za ta mutunta umarnin kotu na farko da ya tabbatar da dakatar da Ganduje a matsayin shugabanta na kasa ba.
A wani labarin, Legit Hausa ta rahoto cewa Abdullahi Ganduje ya yi wa gwamnatin jihar Kano shagube da cewar "kujerar APC tana kan Ganduje ne, kuma zama daram dam."
Ganduje ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu ne ya tabbatar masa da shugabancin APC, yayin da ake ta takaddamar tsige shi daga kujerarsa ta shugaban jam'iyyar na kasa.
Asali: Legit.ng