Home Back

Ƙungiyar ɗaliban Sakandiren Gwale GOBA, aji na 1984, ta ƙudiri aniyar ci gaba da tallafawa makarantar

dalafmkano.com 2024/5/17

Shugaban kungiyar ɗaliban makarantar sakandare ta Gwale GOBA, aji na 1984, Muhammad Mukhtar Idris, ya jaddada aniyar su na ci gaba da tallafawa makarantar a fannoni daban-daban, domin ƙara ɗaga darajar ta.

Muhammad Muhktar ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen taron shan ruwan da kungiyar ta saba gabatarwa a kowacce shekara, haɗi da cikar kungiyar shekaru 40 da kafuwa, wanda ya gudana a ƙarshen makon nan,

Ya kuma ce manufar shirya taron shine domin su sadar da zumunci a tsakaninsu, tare kuma da duba hanyoyin da za su kara taimakawa makarantar, da kuma marasa lafiya da iyalan mabobin su da suka rasu.

Mallam Abdullahi Dawakin kudu, guda ne daga cikin tsofaffin daliban makarantar, ya ce taron ya da aka shirya ya sa sun haɗu da mutanen da suka daɗe basu haɗu da su ba, inda suka sada zumunci a tsakanin su.

Yayin taron ƙungiyar ta kuma karrama wasu daga cikin tsofaffin daliban makarantar, sakamakon gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban kungiyar da ma makarantar ta sakandiren Gwale, da ke jihar Kano.

People are also reading