Home Back

An Cafke Ɗan Majalisa da Basarake Kan Zargin Daukar Nauyin Ta’addanci a Zamfara

legit.ng 2024/6/29
  • Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta ce ta kama wani dan majalisar jiha, hakimi da kuma tsohon shugaban karamar hukuma
  • Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Muhammad Dalijan ya ce an kama manyan mutanen ne bisa zargin su da daukar nauyin ta'addanci a jihar
  • CP Muhammad Dalijan ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin tawagar Majalisar Dinkin Duniya kan yaƙi da ta'addanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Gusau, Jihar Zamfara - Rahotanni na nuni da cewa rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta cafke wasu manyan mutane bisa zargin su da daukar nauyin ta'addanci a jihar.

Majalisar Dinkin Duniya ta kai daukin tsaro a Zamfara
Zamfara: An kama dan majalisa da hakimi kan zargin daukar nauyin ta'addanci. Hoto: Legit.ng Asali: Original

An kama manyan mutane a Zamfara

Daga cikin wadanda aka kama akwai wani ɗan majalisar jihar, hakimi da kuma tsohon shugaban karamar hukuma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan 'yan sandan jihar Zamfara, Muhammad Dalijan ne ya bayyana hakan a hedikwatar rundunar sa ke Gusau, in ji rahoton Channels.

CP Muhammad Dalijan ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin jami'in da ke kuka da rundunar yaki da ta'addanci, karkashin ofishin UN na UNODC, Thomas Parker.

Sai dai an ce kwamishinan 'yan sandan bai bayyana sunayen manyan mutanen da aka kama bisa daukar nauyin ta'addanci a jihar ba.

An roki UN ta gina cibiyar gwaje-gwaje

CP Dalijan ya kuma roki Majalisar Ɗinkin Duniya da ta gina cibiyar gwaje-gwaje na binciken ayyukan ta'addanci a Zamfara domin takaita wahalhalun zuwa Legas.

A yayin da Dalijan ya karbi bakuncin Park, ya nemi UN da ta aiwatar da irin ayyukan da ta yi a Maiduguri a nan Zamfara.

Game da matsalar tsaro a Zamfara, kwamishinan ya ba UN tabbacin ta'addanci ya ragu sosai a jihar saboda kokarin jami'an tsaro na kama 'yan ta'adda da kakkabe wasu.

UN ta amsa rokon gwamnatin Zamfara

Da ya ke jawabi, Parker ya ce sun je jihar Zamfara ne domin amsa rokon da Gwamna Dauda Lawal ya yi wa UN na ba jihar gudunmawa wajen yaki da matsalar tsaro.

Parker ya shaidawa 'yan sandan cewa UN na a shirye domin yin nazarin matsalar tsaron jihar da kuma samar da hanyar magance ta gaba daya.

Ofishin UNDOC na Majalisar Dinkin Duniyar ya kaddamar da tattaunawar kwanaki uku da masu ruwa da tsaki a jihar domin magance matsalolin tsaro da suka addabi yankin.

'Yan daba sun kashe soja a Kaduna

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu 'yan daba da ake kyautata zaton masu kwacen waya ne sun kashe wani sojan Najeriya a jihar Kaduna.

An ce masu kwacen wayar sun kashe sojan mai suna Laftanar I.M Abubakar a Unguwan Sarki da ke cikin birnin jihar a hanyarsa ta komawa gida.

Asali: Legit.ng

People are also reading