Home Back

Tsarin Tazarar Haihuwa Mara Amfani Da Magani (2)

leadership.ng 2024/7/1
Tsarin Tazarar Haihuwa Mara Amfani Da Magani (2)

Ci gaba daga makon jiya

Dalilin rashin maniyyin bayan kwan ya lalace ya fita su kuma wadancan jijiyoyi da suka tara jini a cikinsu, sai su yi wani abu da ake kira fushi, ba su ji dadi ba, a dalilin haka sai suke kartar jikin mahaifar mace, sai ka ji mace tace maka tana yawan fama da ciwon mara (lower abdominal pain) musamman idan ta gama Haila. A nan za mu fahimci rashin aure na daga abin da ke jawo wannan, kuma maganin haka shi ne aure duk da akan samu masu auren ma su fuskanci hakan.

Idan karce jijiyoyin nan ya yi yawa kuma aka yi rashin sa’a sai su fashe, idan kuma suka fashe sai jini ya yi ta fita ba tsayawa a wasu, wannan shi ne ake kira da jinin Istihada, daman Manzon Allah (SAW) ya taba gayawa wata mata cewar ai wannan jinin na jijiya ne. Toh daga nan ne kuma injinin ya fice.

Dan haka idan Mace me aure ce kuma tana son yin ‘family planning da Mijinta, to hanya mafi sauki itace;

kamar yadda muka ji bayan gama hailar ta da kwanaki 14 ake sakin wadancan kwayaye zuwa mahaifa, kuma sukan yi kwanaki 2 kafin su mutu, shi kuma maniyyin namijin yakan yi kwanaki 3 kafin ya mutu, To su ma’auratan ka da su yi jima’i tun ranar 11 da gama hailar ta, har sai bayan ranar 17 da gama hailarta.

Ku dan tsaya kadan a nan kafin ku ci gaba ku yi tunanin me ya sa na ce haka?

Dalilin hakan kuwa shi ne; ranar 14 kwoi ke zuwa, to idan suka sadu ranar 12, ka da mu manta Maniyyi sai yayi kwanaki 3 kafin ya mutu, to kun ga idan suka sadu ranar 12, maniyyin namijin na nan a mahaifar a raye har ranar 14 da za a saki kwan, zai zauna na tsawon kwanakin 12,13,14 kafin ya mutu, to kun ga za su ci karo ranar 14, kuma babu abin da zai hana shi sarrafa kwan nan.

An ce kar ku sadu har sai bayan ranar 17 ne saboda shi kuma kwan yakan yi kwanaki 2 kafin ya mutu. To wadannan kwanaki 5 din-12,13,14,15 ,16 da gama Hailar mace, su ake kira da ‘DANGER PERIODS’ Ma’ana kwanaki masu hatsari, an kira su da haka ne saboda idan dai aka sadu da Mace a wadannan kwanakin to kuwa tabbas za ta samu ciki, sai dai idan Mulkin Ubangiji ya shigo ciki ko kuma in dama cikin ma’auratan akwai larurar da ke hana daukar ciki.

Amma idan har ma’aurata na son yin ‘family planning’ ba tare da sa ko shan komi ba wadannan kwanakin za su kauce wa saduwa a ciki wato tun daga ranar 11 da gama haila har sai ranar 17 da gama haila kuma sati 1 kenan.

Sannan kuskuren da kan faru wasu na zuwa da sunan a sadun amma in ya ji zai kawo sai ya zare. Ina mai tabbatar ma wannan ruwan me santsi na maniyyi da kan fara fitowa ka zaci maziyyi ne shi kansa ya wadatar ya sa ciki ya shiga domin akwai maniyyi daga karshensa. Wannan ta sa ‘yan matan dakan auka tarkon samari ke karewa da ciki a zaton ba a yi ‘release’ jikinsu ba, don haka in dai za a yi to a kiyayi kusanta kurum.

Kuma irin hakan ya sa ba a ba hanyar inganci 100% ba domin ko ya maniyyi yake ya wadatar. Haka kuma wasu matan duk sati 3 suke haila don haka kwanakin fara ‘obulation’ dinsu ba zai kai har 14 ba, galibi bayan kwana 10 ‘obulation’ na iya faruwa, kun ga ita sai dsi a kaurace mata kwanaki 8 zuwa 13 kenan.

Sannan wani abu; a yayin da kwai din can ke tafiya a cikin ‘FOLLOPIAN TUBE’ daga obary zuwa cikin mahaifa idan ya makale a hanya kuma aka zo aka sadu da mace toh shi ne maimakon ciki ya kasance a cikin mahaifa sai ya kasance a wajen mahaifa wanda shi muke kira ‘ECTOPIC PREGNANCY’ wanda dole sai dai a yi aiki a cire.

Kuma wannan ‘fallopian tube’ din ya samu matsala kenan har abada. Sai dai da yake biyu ne, to daya ya isa ta sami ciki da shi, wata hikima ta Allah shi ya sa ya yi biyun… to in ko duk biyun suka tabu aka kuma samun ‘ectopic’ tofa shi ne ciki sai dai a yi ma mace dashensa gaskiya ba za ta iya dauka ba.

Wanda ‘Pelbic inflammatory disease’ na daga kan gaba abin da ke jawo tangardar ‘Fallopian tube’ din, don haka mata ku daina sake da ‘infection’, a kuma daina amfani da wani maganin matsi ko tsarki da ruwan sassake-sassake, in kun ki kuma to jiki magayi, ke da haihuwa kya zo sai dai ki ji a makwabta ko awakan layinku na yi, a kuma lura da tsafta.

People are also reading