Home Back

Gwamnatin Gombe Za Ta Yi Tituna da Kilomita 1 Za Ta Lakume Sama da Naira Biliyan 1

legit.ng 2024/7/6
  • Gwamnatin jihar Gombe ta sanar da fara ayyukan tituna masu tsawon kilomita 18.5 a kwaryar jihar da za su lakume bilyoyi
  • Gwamna jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce ya kammala ware Naira biliyan 20 domin yin titunan
  • Sai dai gwamnatin ta yi karin haske kan cewa kudin da za a kashe zai shafi gyara wasu titunan da suke wajen kwaryar jihar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe- Gwamnatin jihar Gombe ta shirya kashe zunzurutun kudi sama da naira biliyan 20 domin yin tituna a jihar.

Kwamishinan ayyuka na jihar, Maijama’a Kallamu ne ya bayyana haka ga manema labarai bayan kammala zaman majalisar jihar.

Gwamnan Gombe
Gwamnati za ta kashe N20b kan tituna a Gombe. Hoto: Isma'ila Uba Misilli. Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar bayan ayyukan titunan kwamishinan ya ce gwamnan zai sayar da taki a farashi mai rahusa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Titin FTH zuwa FCE (T) Gombe

Daga cikin titunan da aikin zai shafa akwai titin da ke kan hanyar asibitin koyarwa na tarayya (FTH) zuwa kolejin ilimi da fasaha da ke Gombe.

Gwamnatin jihar ta ce za a biyunta titin ne saboda yawan cunkoso da yake haifarwa ga abubuwan hawa.

Gyaran titin Dukku zuwa Dokoro

Har ila yau gwamnatin za ta kashe Naira biliyan 1.5 a gyaran titin Dukku zuwa Dokoro da ke karamar hukumar Dukku.

Kwamishinan ayyuka na jihar ya shaida cewa za a gyara magudanar ruwa shida da ruwan sama ya lalata a kan hanyar.

Gwamnan Gombe zai samar da taki

Gwamnan jihar ya bayyana cewa zai samar da taki ga manoma a farashi mai rahusa domin bunkasa noma.

Cikin sakon da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Isma'ila Uba Misilli ya wallafa a shafin sa na Facebook ya nuna cewa za a sayar da buhun taki ne a N22,000 yayin da farashin kasuwa ya ke a N45,000.

Mahajjata sun yi zanga zanga a Makka

A wani rahoton, kun ji cewa masu mahajjatan Najeriya sun gudanar da zanga-zanga a Saudiyya biyo bayan samun matsala da aka yi kan guzurinsu.

Mahajjatan da suka taso daga Abuja sun ce hukumomi sun rage musu kuɗin guzurin da suka musu alƙawari za su ba su idan sun isa Makka.

Asali: Legit.ng

People are also reading