Yawaitar kai wa dalibai hari ya tayar da hankalin mahukuntan Faransa
Wani dalibi mai kimanin shekaru 15 ya rasa ransa a Faransa sakamakon raunukan da ya samu, bayan dukan kawo wukan da wasu suka lakada masa.
Wallafawa ranar: 06/04/2024 - 16:48
Minti 1
Bayanai sun ce a ranar Alhamis din da ta gabata ne gungun wasu matasa suka yi masa rubdugun a kusa da makarantarsa da ke kudancin birnin Paris, lamarin da ya janyo masa bugun zuciya, wanda kuma bayan garzayawa da shi asibiti ya mutu a ranar Juma’a.
Karo na biyu kenan cikin mako guda da aka aikata irin wannan cin zali a Faransa, inda a ranar Talata, wata daliba mai shekaru 13 ta shiga dogon suma bayan dukan da wasu suka lakada mata a harabar makarantar da take zuwa a birnin Montpellier.
Wadannan lamurra na zuwa ne a yayin da hankalin mahukuntan Faransa ya tashi biyo bayan yawaitar sakwannin barazanar kai wa matsa hari da ake aikewa da su a makarantu da dama.
Domin shawo matsalar ce ma, shugaban Emmanuel Macron ya ce dole a dauki matakan bai wa makarantun kasar kariya daga wannan barazana.
A nata bangaren, rundunar ‘yan sandan Faransa ta sanar da kama wani matashi mai shekaru 17, bisa tuhumarsa da hannu a mutuwar dalibin baya bayan nan da aka kashe.