Home Back

Shugaba Ramaphosa ya bayyana ministocin gwamnatin haɗaka a Afirka ta Kudu

bbc.com 2024/10/6
Cyril Ramaphosa

Asalin hoton, EPA

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana sabuwar majalisar ministocin kasar ta hadaka, wata daya bayan da jam’iyyarsa ta ANC, ta kasa samun rinjayen da ake bukata a zaben majalisar dokoki da aka yi a watan Mayu.

Babbar jam’iyyar hamayya ta Democratic Alliance ta samu mukami shida da suka hada da na ministan gona, wanda jagoranta John steinheusen zai rike.

Sai jam'iyyar Zulu Nationalist Inkatha Freedom, da wasu kananan jam'iyyu za su raba sauran mukaman ministoci shida.

Jam'iyyar DA ta sanar da shirin raba mukaman gwamnati kan gundumomi 9 da ake da su domin magance tashe-tashen hankali.

An cimma wannan matsaya ne a karshe bayan makonni da aka shafe ana ta sa-toka-sa-katsi a tattaunawar kafa gwamnatin hadakar, lamarin da ya yi barazanar rushewar gamayyar.

Shugaba Ramaphosa, ya ce sabuwar gwamnatin za ta bayar da fifiko ne a kan tabbatar da bunkasar tattalin arzikin kasar ta Afirka ta Kudu tare da mayar da hankali wajen yakar fatara da talauci da kuma bambanci a tsakanin al’umma.

Sabuwar majalisar ministocin ta gwamnatin hadaka da shugaban ya sanar, ta samu karin ministoci fiye da a baya, inda aka yi hakan domin ganin jam’iyyu 11 da ke cikin hadakar kowacce ta samu shiga.

Sai dai mukaman ministocin manyan ma’aikatu za su ci gaba da kasancewa karkashin ikon jam’iyyar Shugaban, ANC.

Mukaman da suka hada da na ma’aikatar harkokin kasashen waje, wadda take goyon bayan fafutukar Falasdinawa.

Akwai kuma ma’aikatar ma’adanai da kasuwanci da kuma ta sauya tsarin mallakar filaye wadda ke dauke da manufofin da ake ce-ce-ku-ce a kansu na karfafa tattalin arzikin bakaken fata.

Ita kuwa babbar jam’iyyar hamayya da ke cikin hadakar, Democratic Alliance, mai manufofi na jari-hujja, za ta yi fama da batun matsaloli na bakin haure, kasancewar ma’aikatar harkokin cikin gida na hannunta.

Haka kuma ita aka danka wa ma’aikatar ayyuka, wadda ta kasance cibiyar cin hanci da rashawa

Mista Ramaphosa ya ce, dukkanin ministocin za su yi aiki ne domin amfani da cigaban dukkanin al’ummar kasar ta Afirka ta Kudu, ba jam’iyyunsu ba.

Shugaban ya kuma yi kira ga dukkanin al’ummar kasar da ta hada hannu a tattaunawa ta kasa domin samun mafita a matsalolin tattalin arziki da kasar ke fama da su.

People are also reading