Home Back

Wahalar Fetur: Fadar shugaban ƙasa kiyi wani abu dan mutane su samu sauƙi – Ƙungiyar Nothern Concern Soliderity

dalafmkano.com 2024/5/19

Yayin da al’umma ke ci gaba da fuskantar wahalar man fetur a ƙasar nan, ƙungiyar da ta damu da abubuwan da suka shafi arewacin ƙasar nan ta Northern Concern Soliderity, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi abinda ya dace dan ganin mutane sun samu wani sauƙi.

Babban jami’in gudanarwar ƙungiyar, kuma sakataren riƙo na zauren gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya, Kwamared Saddat Usman Maiyaƙi, ne ya bayyana hakan a zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, lokacin da yake nuna takaici kan irin wahalar da al’ummar ƙasa suke sha wajen shan man Fetur a gidajen man.

Ya ce duba da halin matsin rayuwar da al’umma suka samu kansu a ciki, akwai buƙatar shugabanni da masu ruwa da tsaki su kawo ƙarshen wahalar man Fetur ɗin da aka fama da ita.

Kwamared Saddat Maiyaƙi, ya kuma haƙurƙurtar da al’ummar ƙasar nan kan halin ƙuncin rayuwar da suka samu kai a ciki, inda ya yi fatan komai ya zo karshe cikin ƙanƙanen lokaci.

People are also reading