Home Back

Ko Iran za ta mayar da martani kan harin Isra'ila da ya kashe mata babban janar?

bbc.com 2024/5/17

Asalin hoton, Reuters

Baraguzan ginin da hari ta sama ya lalata a Damascus
Bayanan hoto, Hari ta saman ya lalata ofishin jakadancin Iran a Damascus
  • Marubuci, Baran Abbasi
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

Iran ta yi alkawarin mayar da kakkausan martani a kan harin saman da aka kai kan ofishin jakadancinta da ke Damascus, babban birnin Syria a ranar Litinin.

Jakadan Iran a Damascus ya ce mutum 13 harin ya kashe ciki har da mambobin sojojin juyin-juya hali na Jamhuriyar musulunci guda bakwai da 'yan kasar Syria shida.

Daga cikin mutanen akwai birgediya janar Mohammad Reza Zahedi, wanda jigo ne a cikin dakarun Kurdawa.

Isra'ila dai ba ta ce komai ba, to amma Syria da Iran sun dora alhakin harin a kanta.

"Wannan hari ne ba wai a kan kasar Iran ba kadai, har da shugabannin sojojin juyin-juya halin Jamhuriyar musuluncin, wadda kuma kisan da aka yi wa babban janar dinsu babban rashi ne ga su dakarun wadanda ke kai wa 'yan Hezbollah makamai a Lebanon da Syria." In ji Fawaz Gerges, farfesa a sashen hulda da jama'a a jami'ar London.

Asalin hoton, Reuters

Shugaban Iran Ebrahim Raisi
Bayanan hoto, Shugaban Iran, Ebrahim Raisi tare da ministocinsa na tattaunawa a kan harin da aka kai

Martanin shugabannin Iran kan harin

Harin dai ya janyo suka daga manyan jami'an Iran da kuma barazanar mayar da martani a kan Isra'ila.

"Za mu mayar musu da martani ta yadda sai sun yi da-na-sanin abin da suka aikata". In ji jagoran addinin Iran Ali Khamenei.

Shi kuwa shugaba Ebrahim Raisi, kiran harin ya yi a matsayin rashin imani da tausayi wanda kuma ba za a amince da shi ba.

Cikin wata tattaunawa da suka yi ta waya tare da takwaransa na Syria, ministan harkokin wajen Iran, Hossein Amir-Abdollahian, ya bayyana harin a matsayin abin da ya sabawa dokokin kasa da kasa.

Ya nuna wa Isra'ila yatsa, inda ministan harkokin wajen Iran din Amir-Abdollahian ya ce firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya samu 'matsala a kwakwalwarsa'.

Ra'ayoyin masana kan martanin Iran

Wadannan kalamai sun sanya fargabar karuwar zaman dar-dar a tsakanin Isra'ila da Iran, to amma kwararru sun shaida wa BBC cewa, martanin da Iran din za ta mayar ba lallai ya yi tasiri ba.

"Iran ba ta da karfin da za ta tunkari Isra'ila bisa la'akari da karfin sojinta da yanayin siyasa da tattalin arzikinta." in ji Ali Sadrzadeh, mai sharihi a kan al'amuran da suka shafi Gabas ta tsakiya.

"To amma ya kamata su yi wani abu wanda a nan gaba ba za a kara kai musu irin wannan hari ba, ko kuma su yi abin da za su kare kansu."

Wannan dai ra'ayin Fawas Gerges ne, wanda ya yi amanna cewa Iran ba za ta iya yi wa Isra'ila komai ba, duk da Isra'ilar ta yi matukar cin mutuncinta.

Gerges ya ce mai yiwuwa Iran ta hakura, saboda ta gwammace fifita manufarta guda ta hada makamin nukiliya.

"Iran na kara samun karfin iko, tana da makamashin uranium, tana samun nasara a wa su abubuwanta.

Yanzu abin da ya kamata Iran ta yi shi ne ba wai ta aike da makamai masu linzami 50 don ta kashe Isra'ilawa 100 ba ne, ta tabbatar ta tsare gidanta ba kawai daga hare-haren Isra'ial ba har ma na Amurka". In ji Gesges.

Tun bayan fara yakin Isra'ila a Gaza, hare-haren makamai masu linzami da na jirage maras matuka da mayakan Hezbollah da ke samun goyon bayan Iran a Syria da Iraqi da Lebanon da kuma Yemen ke kai wa a kan Isra'ila ke kara karuwa, to amma kamar sun takaita ayyukansu na takalar Isra'ilan.

To ko akwai yiwuwar 'yan Hezbollah wadanda suka saba musayar wuta da Isra'ila za su mayar da martani a kan harin Damascus?

Asalin hoton, AFP

Mayakan Hezbollah
Bayanan hoto, Mayakan Hezbollah

Ko Iran za ta yi amfani da Hezbollah?

Hezbollah na daya daga cikin kungiyoyin da ke da manyan makamai da kuma mambobi, wani kiyasi da aka yi ya nuna cewa kungiyar na da mambobi tsakani dubu 20 da dubu 50, kuma yawancinsu sun samu horo sosai.

Bugu da kari, kungiyar na da akalla makaman roka dubu 130 da masu linzami da dama.

Kwararrun da BBC ta tattauna da su sun ce ba lallai ba ne kungiyar ta kaddamar da wani babban hari kan Isra'ila ba.

"Hezbollah ba ta son ta fada tarkon Isra'ila saboda ta fahimci cewa Benjamin Netanyahu da kuma 'yan majalisar na duba yiwuwar fadada yaki da suke.

Makomar siyasar Benjamin Netanyahu ta dogara ne a kan ci gaba da yakin da ake a Gaza sannan yakin na karuwa a arewacin Gaza inda ake gwabzawa da 'yan Hezbollah da kuma Iran din kanta." in ji Fawaz Gerges.

Ali Sadrzadeh, ya yi amanna cewa akwai yiwuwar Iran ta dan mayar da martani mai makon ta shiga yaki da Isra'ila.

"Iran ta kware wajen kai manyan hare-hare kamar irin wanda ta kai a matsayin martani bayan da aka kashe mata babban kwamandanta, Qasem Soleimani." in ji Sadrzadeh, yana mai bayar da misali da harin makami mai linzamin da Iran ta kai wa sansanin Al Asad a Iraq a ranar 8 ga watan Janairun 2020.

Iran ta kai hari sansanin Al Asad domin mayar da martani a kan wani hari da Amurka ta kai da jirgi maras matuki Bagadaza da ya yi sanadin mutuwar babban kwamandanta Qasem Soleimani.

Asalin hoton, Security media cell via EPA

Mota na cin wuta
Bayanan hoto, An kashe babban janar din Iran Qasem Soleimani a watan Janairun 2020

Duk da alkawarin Iran na daukar babbar fansa a kan kisan, babu wani sojan Amurka da ke sansanin da aka kashe, sannan akwai rahotannin da ke cewa an gargadi sojojin Amurkan a kan yiwuwar kai harin ramuwar gayya.

Fawaz Gerges, ya yi amanna cewa harin da aka kai kan ofishin jakadancin Iran a Damascus na nufin wata dabarace ta nuna gazawar bangaren tsaron Iran.

Yousof Azizi, mai bincike ne a kwalejin fasaha da ke Virginia, ya ce za a ci gaba da samun banbancin ra'ayi a kan ko Iran za ta nuna karfinta a kan makamin nukiliya wajen mayarwa da Isra'ila martani a kan harin da aka kai mata.

Asalin hoton, Reuters

Wani mutum tsaye a wajen ofishin jakadancin Iran da aka kai wa hari a Damascus
Bayanan hoto, Wani mutum tsaye a wajen ofishin jakadancin Iran da aka kai wa hari a Damascus

Idan Iran ba ta dauki matakin soji ba, to me za ta yi?

"Ba za mu yanke hukunci cewa Iran ba za ta yi komai ba, za ta iya kai hare-hare ta intanet wajen daukar fansa a kan Isra'ila, ma'ana ko su yi amfani da yin kutse ta hanyoyin fasahar sadarwar Isra'ila su samu wasu bayanai da Isra'ila ba ta son a sani wanda idan ta yi hakan ta yi ramuwar gayya ta wani salo na daban." In ji Yousof Azizi.

Yanzu dai ya rage wa Iran da kuma jagoran addininta su yanke shawara a kan matakin da ya kamata kasarsu ta dauka domin share kunya da kuma yin kan-da-garki ga hare-hare a nan gaba.

To amma a yanzu mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Iran, Naseer Kanani,shi kadai ya san abin da ke ransa.

"Iran na da damar mayar da martani don haka a yanzu za ta yanke shawara a kan irin martanin da ya kamata da kuma hukuncin da ya kamata." In ji ministan, a wani gargadin da ya yi bayan afkuwar al'amarin.

People are also reading