Home Back

Sukar Gwamna Uba Sani Ya Sanya Ta Hannun Daman El-Rufai Shiga Komar DSS

legit.ng 2024/5/19
  • Wata ƴar siyasa ta jam'iyyar APC a jihar Kaduna ta faɗa hannun hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS)
  • Jami'an hukumar sun yi caraf da Aisha Galadima wacce ta hannun daman Nasir Ahmad El-Rufai ce bayan ta caccaki Gwamna Uba Sani
  • Sai dai, gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa ba ta da masaniya kan kamun da aka yi wa ƴar siyasan ta jam'iyyar APC

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Jami'an hukumar DSS sun cafke wata ƴar siyasa ta jam'iyyar APC, Aisha Galadima, a jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an cafke ƴar siyasar wacce ta hannun daman tsohon gwamnan jihar, Nasir Ahmad El-Rufai ce a ranar Lahadi, 14 ga watan Afirilun 2024.

DSS ta cafke ta hannun daman El-Rufai
An cafke Aisha Galadima bisa zargin sukar Gwamna Uba Sani Hoto: @ubasanius, @elrufai Asali: Twitter

Rahoton jaridar Leadership ya nuna cewa kamun da aka yi mata nada nasaba da wani rubutu da ta yi a soshiyal midiya kan gwamnan jihar Malam Uba Sani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar majiyoyi, Aisha Galadima ta caccaki Gwamna Uba Sani bisa kalaman da ya yi kan Nasir El-Rufai, a shafinta na Facebook.

Wani maƙwabcinta ya bayyana cewa an cafke ta ne a gidanta da ke unguwar Tudun Wada a Kaduna a ranar Lahadi, yayin da wata ƙawarta ta ce an kashe wayoyinta bayan kamun da aka yi mata.

Gwamnati na da masaniya kan kama Aisha?

Sai dai, babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan Kaduna, Muhammad Lawal Shehu, ya ce baya da masaniya kan kamun da aka yi mata.

Ya yi nuni da cewa a tuntuɓi hukumar tsaron farin kaya ta DSS domin samun ƙarin bayani kan lamarin.

A kalamansa:

"Ba ni da masaniya cewa an kama wata mata saboda ta caccaki mai girma gwamna. Koma dai menene ku tuntuɓi hukumar DSS ba gwamnatin jihar Kaduna ba."

Yaron El-Rufai ya soki Uba Sani

A wani labarin kuma, kun ji cewa yaron tsohon gwamnan jihar Kaduna, Bashir Nasir El-Rufai, ya caccaki Gwamna Uba Sani kan batun bashin da ya ce ya gada a wajen El-Rufai.

Bashir ya yi nuni da gwamnan na ƙoƙarin fakewa ne da gaza taɓuka komai da ya yi tun bayan hawansa mulki.

Asali: Legit.ng

People are also reading