Home Back

RIKICIN CINIKIN MAKAMAI TSAKANIN NAJERIYA DA AMURKA: An riƙe wa Najeriya Dala miliyan 8.6, an ɗaure dillalin makamai a Kurkukun California

premiumtimesng.com 2024/5/15
RIKICIN CINIKIN MAKAMAI TSAKANIN NAJERIYA DA AMURKA: An riƙe wa Najeriya Dala miliyan 8.6, an ɗaure dillalin makamai a Kurkukun California

Ja-in-ja, sa-toka-sa-katsi da sa-in-sa sun ɓarke tsakanin Najeriya da Amurka, a ƙoƙarin da Najeriya ke yi na ganin ta karɓo kuɗin ta har Dala miliyan 8.6, waɗanda gwamnatin Amurka ta ƙwace tun cikin 2015.

Tun bayan ƙwace kuɗaɗen dai Amurka ta ƙi sakin kuɗin bisa dalilan cewa an nemi a sayi makaman ba bisa ƙa’idar da doka ta gindaya ba.

Tun da farko dai Najeriya ta biya kuɗin ta hannun wani kamfanin dillacin makamai na Amurka, mai suna Dolarian Capital Inc (DCL), cikin 2014, domin sayo makamai a Amurka, bayan ‘yan Boko Haram sun sace ɗaliban Chibok su 276, a Jihar Barno.

Sai dai kuma an samu tangarɗa yayin da Gwamnatin Amurka ta ƙi rattaba wa DCI hannun amincewa ya yi wa Najeriya dillacin makaman da kuma aika su Najeriya.

Nan da nan sai Gwamnatin Amurka ta garzaya kotu, inda kotu ta bada sammacin ƙwace kuɗaɗen, bisa dalilan cewa cinikin ya karya dokar Cinikin Makamai Tsakanin Amurka da Ƙasashe.

Wani dalilin da gwamnatin Amurka ta bayar kuma shi ne, kamfanin DCI ba shi da lasisin shiga cinikin makamai, shigo da su ko fitar da makamai zuwa wasu ƙasashe.

Kotun Gundumar Gabacin Califoniya ce ta bada waranti da sammacin ƙwace kuɗaɗen, waɗanda a lokacin aka kimshe su cikin asusun bankuna daban-daban.

An ƙwace kuɗaɗen a ranar 2 ga Fabrairu, 2015.

Cinikin Makamai: Yadda Amurka Ta Ɗaure Dillalin Cinikin Makaman Najeriya:

Gwamnatin Amurka ta maka mai kamfanin DCI, mai suna Ara Dolarian kotu. Ana caje shi da laifin karya dokar cinikin makamai, domin ba shi da lasisin amincewa ya yi cinikin duk wani nau’in kayan da sojoji ke amfani da su.

Cikin Janairu 2020, Dolarian ya amsa laifin sa, kuma kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin watanni 14 a ranar 2 ga Maris, 2023.

Tuni dai aka tura shi gidan kurkuku na Lampoc, wanda ke California.

Rikicin Haƙƙin Mallakar Kuɗaɗen Makamai Tsakanin Najeriya Da Amurka:

Cikin watan Yuni, 2015, gwamnatin Amurka ta nemi kotu ta haramta maida wa Najeriya kuɗaɗen.

Ita kuwa Kotun California ta bada sammacin ƙwace kuɗaɗen, aka damƙa wa gwamnatin Amurka su.

To a yanzu Najeriya ta sa himma a kotu, ta na neman kotu ta soke umarnin da aka amince Amurka ta ƙwace kuɗin, kuma a maido wa Najeriya abin ta.

Amurka dai ba ta ce ba kuɗin Najeriya ba ne, amma kuma ta na kawo cikas wajen ganin an maida wa Najeriya kuɗin.

Cinikin Makamai: Lauyan Najeriya Da Na Amurka Na Fesa Wa Juna Zafafan Kalmomin Turanci:

Tun cikin 2021 Najeriya ta fara gaganiyar ganin an dawo mata da kuɗin tunda ba a sayar mata da makaman ba.

Najeriya ta ɗauki hayar wani lauya Ba’Amurke, mai suna Jovi Usude, domin shigar mata kokawar ƙwato kuɗin.

Wasu takardun shari’ar da ake kafsawa a kotu, sun faɗo hannun PREMIUM TIMES, masu nuni kan yadda ake jayayya da sa-in-sa tsakanin lauyoyin ɓangarorin biyu, na Najeriya da na Amurka, musamman Antoni Janar na Amurka, Jeffery Spivak, tsawon shekaru biyu. Amma har yanzu sai dawurwura, dabur-dabur da dambarwa ake yi, Najeriya ba ta san matsayin ta a batun ba.

A ƙarshe a ranar 3 ga Yuni, 2023, sai Najeriya ta shigar ga Mai Shari’a na Kotun Gundumar Gabacin California.

Usude lauyan Najeriya, ya nemi a sakar wa Najeriya kuɗin ta, “ba kuɗin wanda aka kama da laifi aka ɗaure ba ne.”

“Saboda lokacin da Najeriya ta ƙulla cinikin makamai da kamfanin DCI, Bai shaida mata cewa ba shi da lasisin shiga dillancin makamai ba.”

Rikicin Cinikin Makamai: Amurka Ta Ƙi Maida Wa Najeriya Dala Miliyan 8.6:

Kwanaki 13 bayan Najeriya ta shigar da ƙorafin ta a Kotun Gundumar Gabacin California, sai Amurka ita ma ta shigar da na ta ba’asin a ranar 20 Ga Yuni, 2023.

Babban Mai Shari’a na Amurka, Spivark, ya shigar da ƙara, ya na so a sake binciken yadda Najeriya ta ƙulla cinikin makamai da DCI, kamfanin da kwata-kwata ba shi da lasisin tu’ammali, dillanci ko safarar duk wasu kayayyakin da sojoji ke amfani da su.”

Yanzu dai a ranar 29 ga Maris, ɓangarorin biyu sun amince a yi binciken kwanaki 90, wanda za a fara sauraren batun a ranar 30 ga Satumba.

Lauyan Najeriya ya shaida irin ƙoƙarin binciken da aka yi a cikin gida, domin tun farko an nemi sayen makaman ne ganin yadda Boko Haram ke kai hare-haren ta’addanci, musamman a Jihar Barno.

Rikicin Cinikin Makamai: ‘An Gano AVM Alkali Mamu Ya Karɓi Cin-hanci, An Ɗaure Shi Shekaru Biyu’ – Lauyan Najeriya:

Lauyan Najeriya ya bada bayanin yadda aka kama Air Vice Marshall Alkali Mamu ya karɓi cin hanci daga Societe d’Equipment Internationaux, har aka ɗaure shi shekaru biyu a kurkuku.

Wannan harƙalla ta kai ga tsare Mashawarcin Musamman Kan Harkokin Tsaro ga Shugaban Ƙasa tsawon shekaru biyar, wato bayanin tsare Sambo Dasuƙi kenan.

People are also reading