Home Back

Hadin Gwiwa Da Sin Ya Ba Matasan Kasashen Afirka Karin Damammakin Raya Kai

leadership.ng 2024/7/5
Hadin Gwiwa Da Sin Ya Ba Matasan Kasashen Afirka Karin Damammakin Raya Kai

A wajen babbar gasar kasa da kasa kan fasahohin sadarwa na ICT da kamfanin Huawei na kasar Sin ya gudanar a kwanan baya a birnin Shenzhen na kasar Sin, wasu kungiyoyi 4 na daliban jami’ar Ibadan da jami’ar fasaha ta tarayya dake Minna (FUTMINNA), sun yi fice daga cikin wasu kungiyoyi fiye da 160, wadanda suka zo daga kasashe da yankuna 49, inda suka cimma manyan lambobin yabo guda 2, da sauran lambobin karramawa 2 dake matsayin farko. Wannan babbar nasarar da suka samu ta nuna cewa, da farko, ba a rasa matasa masu kwarewa a Najeriya ba. Kana na biyu, hadin gwiwar da ake yi tsakanin Sin da Afirka na samar da damammakin nuna kwarewa da raya kai ga matasan Afirka.

Hakika kasar Najeriya, da sauran kasashen dake nahiyar Afirka, za su iya cin gajiyar dimbin al’ummar da suke da su, ta hanyar daukar wasu matakan da suka dace. An ce, zuwa shekarar 2050, yawan al’ummar nahiyar Afirka zai kai 1/4 na daukacin al’ummar duniya, kana fiye da rabinsu za su kasance kasa da shekaru 25 da haihuwa. Wannan yanayi ya sa kasashen Afirka bukatar karfafa kwarewar matasa, da samar musu da isassun guraben aikin yi, ta yadda dimbin al’ummar da ake samu a nahiyar za ta iya zama tushen ci gaban tattalin arzikinta.

A nata bangare, kasar Sin ta lura da bukatun da ke akwai a kasashen Afirka, kuma tana son ba da taimako. Cikin yarjeniyoyin da kasar Sin ta kulla tare da kasashen Afirka a shekarun nan, horar da matasa wani bangare ne mai muhimmanci. Kana a shekarar 2023, Sin ta gabatar da shirin hadin gwiwa da Afirka a fannin horaswa da samar da kwararru, wanda ya kunshi cikakken shirin taimakawa kasashen Afirka samun kwararru, wadanda suke iya kula da harkokin kasa ta hanyar fasahohin zamani, da raya tattalin arziki da zaman al’umma, da binciken kimiyya da fasaha, da kyautata zaman rayuwar jama’a.

To, an samu shiri, amma ta yaya ake aiwatar da shi? Za mu samu amsar ta hanyar duba wasu al’amuran da suka faru a kwanan nan. Ban da gasar ICT da na ambata, a watan da ya gabata, an yi bikin mika wani bangare na jami’ar sufuri ta tarayyar Najeriya, da wani kamfanin Sin ya zuba jari da daukar nauyin gina ta, wadda ta kasance jami’ar sufuri ta farko a nahiyar Afirka. Sa’an nan, a kwanan baya, an kaddamar da shirin hadin gwiwa na “hanyar siliki” a birnin Lagos, wanda ke da niyyar tura wasu hazikan daliban Najeriya zuwa kwalejojin kasar Sin don samun horo a fannin fasahohin sana’a, ta yadda za su zama kwararru a fannonin hada motoci da na’urorin sanyaya daki na AC, da kasar Najeriya ke bukata. Ban da haka, a kasar Madagascar, an kaddamar da wata sabuwar makarantar koyar da fasahohin sana’a mai taken “Luban Workshop” da kasar Sin ta ba da tallafi, yayin da a birnin Beijing na kasar Sin, aka kammala wani kwas da aka shirya ma jami’an gwamnatocin kasashen Afirka kan dabarar rage talauci, wanda ya kasance irinsa na farko… Duk wadannan abubuwan da suka faru a kwanan nan sun nuna yadda ake kokarin gudanar da hadin kai tsakanin bangarorin Sin da Afirka a fannin samar da kwararru.

Sa’an nan kokarin da kasar Sin ta yi a wannan fanni ya sa ta samun yabo. Darektan cibiyar ba da shawara kan manufofin kasashen Afirka da kasar ta Sin ta kasar Ghana, Paul Frimpong, ya ce, tallafin da kasar Sin ta ba kasashen Afirka a fannin koyar da fasahohin sana’a ya riga ya zama wani muhimmin bangare na yunkurin zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin, wanda ya taka muhimmiyar rawa a kokarin samar da kwararrun ma’aikatan da kasashen Afirka ke bukata. Kana a nasa bangare, Nama Didier, jami’i mai sa ido kan aikin koyo da koyar da harshen Sinanci na ma’aikatar kula da ilimin daliban makarantun sakandare ta kasar Kamaru, ya yabawa shirin da kasar Sin ta gabatar na gudanar da hadin gwiwa tsakanin bangarorin Sin da Afirka don samar da kwararru. A cewarsa, shirin zai iya karfafa ma matasan kasashen Afirka kwarewar aiki, da taimakon kasar Sin wajen mika fasahohin zamani ga kasashen Afirka.

Watakila za ku yi tambaya cewa, me ya sa kasar Sin ke son taimakawa kasashen Afirka samun kwararru? Dalilin ya shafi akidar kasar Sin a fannin hadin gwiwa tare da kasashen Afirka, wato “Rikon gaskiya, da nuna kauna, da sahihanci, gami da samar da hakikanin sakamako”. Wannan tunani na nufin cewa, kasar Sin na fatan ganin samun ci gaban al’umma a kasashen Afirka, kana tana kokarin tabbatar da hakan. Cikin sauki za a iya fahimtar cewa, idan babu isassun kwararrun ma’aikata a kasashen Afirka, to, ta yaya kamfanonin Sin fiye da dubu 10 da suke zuba jari a Afirka za su iya samun biyan bukatarsu ta ma’aikata? Idan dai babu isassun kwararru a Afirka, to, wa zai kula da dimbin kayayyakin more rayuwa da kamfanonin Sin suka zuba jari suka kuma gina su a kasashen Afirka?

Saboda haka za mu san cewa, babbar moriyar kasashen Afirka ta fuskar raya kasa daya ce da ta kasar ta Sin, wadanda ba za a iya raba su ba. Kana har kullum bangarorin 2 suna kokarin hadin gwiwa da juna don tabbatar da moriyarsu ta bai daya. Wannan shi ne dalilin da ya sa kasar Sin ke rikon gaskiya a kokarinta na raya kasashen Afirka, tare da samar da karin damammakin raya kai ga matasan kasashen Afirka. (Bello Wang)

People are also reading