Home Back

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar Rarara, kwana biyu bayan taron Gwamnonin Arewa maso Yamma kan tsaro a Katsina

premiumtimesng.com 2 days ago
Ƴan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar Rarara, kwana biyu bayan taron Gwamnonin Arewa maso Yamma kan tsaro a Katsina

Gungun ‘yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun yi shigar-sunƙuru cikin ƙauyen Kahutu, suka ɗauki Halima Adamu, mahaifiyar mawaƙi, Dauda Kahutu Rarara.

Rahotanni daga wasu kafafen yaɗa labarai da suka haɗa da Taskar Gizago da Daily Trust sun tabbatar da afkuwar mummunan labarin.

Maharan sun yi awon-gaba da Hakima daga gidan ta da ke ƙauyen Kahutu, cikin Ƙaramar Hukumar Ɗanja, ƙaramar hukumar tsohon Gwamnan Katsina, Bello Masari.

Majiyoyi daga ƙauyen Katuhu sun tabbatar wa wasu manema labarai cewa maharan sun shiga ƙauyen wajen ƙarfe 1 na dare ranar Alhamis, wayewar garin Juma’a, ba su tsaya ko’ina ba, sai gidan mahaifiyar Rarara, kuma suka tasa ta a gaba.

“Mahara sun shigo ƙauyen a ƙasa, kuma ba su yi harbi ko sau ɗaya ba. Cikin ‘yan mintina suka yi gaba da ita.

“Gyatumar ba ta nuna masu tirjiya ba, a lokacin da suka umarce ta cewa ta tashi su tafi da ita.

“Duk da cewa maharan sun samu mutane a cikin gidan, amma mahaifiyar Rarara kaɗai suka tafi da ita. Kuma ba wanda ya yi ƙoƙarin tunkarar ‘yan bindigar, soboda ɗauke suke da manyan bindigogi.

“Mai yiwuwa sun ajiye baburan su nesa da garin, suka yi tattaki ƙasa har cikin ƙauyen.”

An dai sace matar kwana uku bayan taron Gwamnatin Arewa maso Yamma kan matsalar tsaro, wanda suka yi a Katsina.

People are also reading