Asalin kwalara da yadda za ku kare kanku daga kamuwa da cutar
Yayin da damuna ke ƙara kankama a Najeriya, Cibiyar Kare Cutuka masu yaduwa ta ƙasar (NCDC) ta ce akwai yiwuwar cutar kwalara ta ci gaba da yaɗuwa tare da yin illa.
Tuni cutar ta hallaka mutum 30 daga farkon shekarar 2024 zuwa tsakiyar watan Yunin shekara, yayin da aka zargin kimanin mutum 1,141 ne suka kamu a ƙananan hukumomi 96 da ke faɗin ƙasar.
Tuni jihar Legas da ke kudancin ƙasar ta bayyana ɓarkewar cutar a cikinta.
Kwalara ƙwayoyin cuta ne da ke yaduwa ta hanyar ruwa, wadda ruwa ko abinci maras tsafta ke yaɗawa.
Kwalara na haifar da gudawa da amai, kuma tana saurin yin kisa idan har ba a ɗauki mataki a kan lokaci ba.
Waɗanda cutar ta yi wa tsanani za su yi fama da rashin ruwan jiki wanda zai kai ga haddasa babbar matsala kuma idan ba a yi gaggawar magani ba mutum na iya mutuwa.
A cikakken bayanin da CDC ta yi kan kwalara ta ce kusan mutum miliyan uku ke kamuwa da cutar duk shekara kuma tana kashe mutum 95,000 duk shekara a duniya.
Ana iya kamuwa da cutar ba tare da nuna wani alamu ba, amma kuma takan iya yin tsanani.
Alƙalumman CDC sun nuna cewa mutum ɗaya cikin 10 da suka kamu da cutar kwalara za ta iya yin tsanani da nuna alamu na amai da gudawa sosai da kuma mutuwar jiki.
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce a wajen ƙarni na 19 kwalara ta bazu a sassan duniya daga Indiya.
Miliyoyin mutane ne suka mutu a sassan duniya sakamakon ɓarkewar annobar sau shida.
WHO ta ce ɓarkewar annobar karo na bakwai ta samo asali ne daga Kudancin Asia a 196, ta bazu zuwa Afirka a 1971 da kuma a yankin Amurka 1991.
Mutum na iya kamuwa da cutar kwalara ta hanyar shan gurɓataccen ruwa ko abinci.
Kuma a lokacin annobar, wanda ya harbu na iya ƙara gurɓata ruwa da abinci.
Cutar kuma na iya bazuwa cikin sauri a yankunan da ba a ɗauki matakan tsaftace ruwan sha da magudanan ruwa ba.
Sai dai kuma Hukumar CDC ta ce yana da wahala cutar ta yaɗu daga wani mutum zuwa wani, don haka mu'amula da wanda ya kamu da kwalara ba ya cikin hatsarin kamuwa da cutar matuƙar za a ɗauki matakin wanke hannu yadda ya kamata.
Mutanen da ke rayuwa a wuraren da babu ruwa mai tsafta da rashin tsaftar muhalli sun fi hatsarin kamuwa da kwalara.
Alamomin kwalara sun haɗa da:
Alamomin sukan ɗauki kwana biyu zuwa uku kafin su bayyana bayan mutum ya harbu da cutar. Wani lokaci yakan kai kwana biyar kafin bayyanar cutar.
Likitoci sukan gudanar da bincike ta hanyar ɗaukar samfurin ba-haya domin gano idan akwai ƙwayar cutar kwalara.
Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa CDC ta ce yawanci ana maganin cutar ne cikin sauƙi ta hanyar bayar da ruwan gishiri a madadin ruwan jiki da mutum ya rasa sakamakon amai da gudawa.
Likitoci suna ba da sinadarin ORS mai ƙunshe da gishiri da suga da ake zubawa cikin gorar ruwa mai tsabta lita ɗaya a bai wa wanda ya harbu da cutar ya sha. Ana amfani da wannan maganin a faɗin duniya.
Idan kuma cutar ta yi ƙamari, za a buƙaci a yi wa mutum ƙarin ruwa.
Idan kuma jariri ne ya harbu da kwalara, za a ba mahaifiyar shawara ta ci gaba da shayar da shi ruwan nono.
Kamar yadda Hukumar daƙile yaɗuwar cutuka ta Najeriya ta bayyana, hanyoyin kare kai daga kamuwa da kwalara su ne: