Home Back

"Akwai Rikitarwa": Fitaccen Lauya Ya Magantu Kan Hukuncin Kotun Game da Sarautar Kano

legit.ng 2024/7/6
  • Yayin da kotu ta yanke hukunci kan rigimar sarautar jihar Kano, lauya kuma Farfesa ya bayyana yadda yake ganin matakin
  • Farfesa Auwal Yadudu ya ce hukuncin kotun abin takaici ne da ba a saba gani na wanda ya bata sunan bangaren shari'a
  • Wannan na zuwa ne bayan hukuncin kotun Tarayya kan dambarwa game da sarautar Kano tsakanin Sanusi II da Aminu Ado

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Fitaccen lauya a Najeriya, Farfesa Auwal Yadudu ya magantu kan hukuncin kotu a shari'ar sarautar Kano.

Yadudu ya ce hukuncin da alkalin ya yanke a jiya Alhamis 20 ga watan Yunin 2024 ya zama daban kuma abin rikitarwa da takaici.

Farfesan ya bayyana haka ne a yayin hira da jaridar Daily Trust inda ya ce bai kamata alkalin ya yi irin wannan hukunci ba.

Ya ce bai dace alkalin kotun da aka karawa girma zuwa Kotun Daukaka Kara ya ɗauki irin wannan mataki ba kan rigimar sarauta.

"Ta yaya zaka ce ka jingine matakan da aka dauka bisa doka, kuma kace baka son shiga lamarin ingancin dokar da aka yi."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk wannan abubuwa za a iya kauce musu, hakan bata sunan bangaren shari'a ne, abin takaici ne kuma hukuncin ya bata sunan alkalin."
"Maganar ko matakin gwamnan ya zo kafin ko bayan umarnin ya danganta ne da hujjoji, ya tabbata daga bayanai dokar ta zo ne daga baya."

- Farfesa Yadudu

Abba ya umarci rushe fadar Nassarawa

Kun ji cewa Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya umarci fitar da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero daga fadar Nassarawa.

Gwamnan ya ba da umarnin ne ga kwamishinan ƴan sanda a jihar, Hussaini Gumel domin fara gyara a fadar Nassarawa.

Asali: Legit.ng

People are also reading