Babbar Sallah: Sarki Sanusi Ya Tura Sakwanni Biyu Ga Kanawa a Ranar Sallah
Jihar Kano - Sarkin Kano na 16, Mohammad Sanusi II, ya yi kira ga Musulmi su rungumi al'adun taimakon mabukata da kuma zaman lafiya a tsakanin juna.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, Sunusi ya ba da wannan shawara ne yayin hudubarsa bayan ya jagoranci sallar Eid a Masallacin Jumu'a na Sheikh Ahmad Tijjani da ke Kofar Mata a Kano.
Sarkin ya jaddada muhimmancin bin koyarwar Annabi Muhammad (SAW), wanda ya jaddada taimakon mabukata, musamman a lokacin bikin babbar sallah.
Haka kuma, ya yi kira ga jama’a su ninka yawan addu’o’insu don samun zaman lafiya a Jihar Kano da kuma kasar nan baki daya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da fama da ake da matsin tattalin arziki a jiha kamar Kano, an lura mutane da dama sun fito domin gudanar da sallar idin bana.
‘Yan Najeriya na ci gaba da fuskantar yanayi mai kunci a fannin tattalin arziki, inda ake ci gaba da bukuwan sallah a cikin matsin tattalin arziki.
Babban abin da ya fi yiwa ‘yan Najeriya ciwo shi ne, yadda kayan abinci ke kara hauhawa da kuma faduwar darajar Naira.
Ana alakanta hakan da sauyin tattalin arziki da kuma tsadar an fetur da aka samu tun bayan da shugaba Tinubu ya janye tallafi a watan Mayun 2023.
A bangare guda, Muhammadu Sanusi II ya gudanar da hawan Sallah domin bukukuwan babbar Sallah.
Sarkin na Kano ya jagoranci sallar idi inda ya yi huduba a masallacin Juma’a na kofar Mata.
An gudanar da Sallar Idi a masallacin Juma'a na Kofar Mata sakamakon ruwan sama da ya mamaye harabar filin Idi wanda hakan ya sanya ba za a iya amfani da shi ba, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Asali: Legit.ng