Home Back

Li Qiang Ya Jaddada Muhimmancin Gina Tsarin Samar Da Ababen Hawa Masu Aiki Da Sabbin Makamashi Hade Da Na’urori Masu Basira

leadership.ng 2024/5/14
Li Qiang Ya Jaddada Muhimmancin Gina Tsarin Samar Da Ababen Hawa Masu Aiki Da Sabbin Makamashi Hade Da Na’urori Masu Basira

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya jaddada muhimmancin gina tsarin samar da ababen hawa masu aiki da sabbin makamashi masu tsafta hade da fasahohin zamani na na’urori masu basira.

Li Qiang ya yi tsokacin ne a Lahadin nan, lokacin da yake duba rumfunan baje kolin ababen hawa na kasa da kasa na birnin Beijing na bana. Ya ce abu ne mai muhimmanci a gina tsarin samar da ababen hawa masu aiki da sabbin makamashi masu tsafta dake hade da na’urori masu basira, kana a daga masana’antun samar da su zuwa matsayin koli, su kasance masu aiki da fasahohin zamani kana marasa gurbata muhalli.

Har ila yau, firaministan na Sin ya yi kira da a kara bunkasa kirkire kirkiren masana’antu, da zurfafa bude kofa da hadin gwiwa, da kara kyautata biyan bukatun masu sayayya da samar da bukatun kasuwanni. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

People are also reading