Home Back

Noma: Gwamnan Zamfara Ya Nemo Masu Zuba Jari Daga Ƙasar Turkiyya

leadership.ng 2024/8/20
Noma: Gwamnan Zamfara Ya Nemo Masu Zuba Jari Daga Ƙasar Turkiyya

Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya samu nasarar jawo hankalin wasu jiga-jigan masu zuba jari ‘yan ƙasar Turkiyya don su zuba jarin su a Zamfara.

A ziyarar da ya kai ƙasar ta Turkiyya a farkon watannan na Yuli, Gwamna Lawal ya samu ganawa da wasu masu zuba jari a ƙasar, tare da kai ziyarorin gani da ido a garuruwa daban-daban.

Kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu yau a Gusau cewa, Gwamna Lawal ya fara wannan ziyarar aiki a ƙasar Turkiyya ne a ranar Lahadi, 30 ga watan Yunin nan da ya gabata, inda ya kwashe kwana shida a can.

zamfara

Sanarwar ta Malam Idris ta kuma bayyana cewa, gwamnan da muƙarrabansa, sun ziyarci wurare da dama, waɗanda suka haɗa da wuraren kayan amfanin gona na zamani, wurin samar da nonon shanu, kiwon kaji da kamfanin ƙera motocin noma (Tarakta) na ‘Turk Traktor (tractors) manufacturing plant.’

“A wannan ziyarar aiki ta Turkiyya, Gwamna Lawal ya fara ne da kai ziyara a Bursa City, inda kamfanin Direkci Group ke da wurin Kayan amfanin gona na zamani mafi girma a ƙasar, inda shugaban kamfanin na Direkci Group, Mehmet Nurullah Direkçi, da kan shi ya zagaya da gwamnan cikin wannan katafaren wuri.

“Shi wannan kamfani na Direkci Group, yana samar da harkokin noma ga ƙasar ta Turkiyya da sauran masu zuba jari ta hanyar kanyan amfanin gona na zamani. Kamfanin zai samar da irin wannan shirin kayan amfanin gona na zamani a jihar Zamfara.

“Idan wannan kamfani na Direkci Group ya shigo Zamfara, zai samar da kayan amfanin gona na zamani kala-kala, waɗanda suka haɗa da noman zamani mara iri, noman zamani mai iri, dashen shuka, noman ayaba na zamani dai sauran harkokin noma na zamani”.

zamfara

Yayin da yake a birnin Gaziantep, Gwamna Lawal ya ziyarci gonar noman madara ta Innova Dairy, wacce ke ba da shawarwari da sabbin hanyoyin kafawa da sarrafa gonakin zamani yadda ya kamata.

“Gonar ta Innova Dairy Farm za ta kafa wani tsari a Jihar Zamfara don amfani da duk fasahohin zamani da suka haɗa da Kiwon Shanu na Zamani, Tsarin Kula da Garken Dabbabi, Tatsar Madarar Shanu, Sarrafa Taki da kayan aikin gona.”

zamfara

A Lardin Sakarya, Gwamna Lawal da tawagarsa sun ziyarci masana’antar sarrafa taraktoci ta TurkTraktor domin tantance tsarin samar da taraktocin da suka dace da noma a Nijeriya.

“A masana’antar Turk Traktor, Gwamna Lawal ya tattauna yiwuwar haɗin gwiwa da kamfanin domin ba iwa Jihar Zamfara damar samun waɗannan taraktoci na zamani.

“Turk Traktor yana da ikon samar da taraktoci ta zamani. Kamfanin dai shi ne kamfani na farko da ke fitar da taraktoci a ƙasar Turkiyya kuma ya kai kashi 88 bisa 100 na adadin taraktocin da ƙasar ke fitarwa a shekarar 2022.

zamfara

“TurkTraktor babban kamfani ne na duniya, wanda ke fitar da taraktoci zuwa ƙasashe 125, kuma yana samar da kusan kashi 80 bisa 100 na adadin kayayyaki zuwa kasuwannin Arewacin Amurka da Turai.”

People are also reading