Home Back

Cika Shekaru 161: Rundunar Sojojin Nijeriya Ta Tallafawa Marayu 400 A Zamfara

leadership.ng 2024/10/5

Cika shekaru 161 da kafa Rundunar Sojojin Nijeriya da irin sadaukarwarta a yayin aiki da tunawa da ranar 'yan mazan jiya.

Cika Shekaru 161: Rundunar Sojojin Nijeriya Ta Tallafawa Marayu 400 A Zamfara

Rundunar Sojojin Nijeriya Brigade ta 1 ta gudanar da bikin murnar cika shekaru 161 da kafa rundunar sojojin Nijeriya tare da marayu da yara marasa galihu da kuma dalibai a jihar Zamfara domin tunawa da ranar sojojin a Nijeriya (NADCEL) 2024.

Wannan muhimmiyar rana an sadaukar da ita ne domin karrama jaruman mu da suka mutu ba tare da son ransu ba domin kare al’ummar ‘yan kasa a yayin gudanar da aiki.

A bikin tunawa da wannan rana, rundunar sojojin Nijeriya Brigade ta 1 da ke Gusau ta gudanar da ayyukan jin kai daban- daban, da suka hada da rabon kayayyakin masarufi, kayan rubutu, tufafi, da rigar kafa ga marayu, marasa galihu, da sauran mabukata a jihar Zamfara.

Birgediya Janar Sani Ahmed, Kwamandan Birgade din ne ya jagoranci rabon kayan sawa ga marayu da mabukata, inda ya jaddada kudirin rundanar sojojin Nijeriya na hada kai da farar hula.

Haka Kuma ya ce wannan shiri dai wani bangare ne na kokarin da Sojoji ke yi na tallafa wa al’ummar farar hula ta hanyoyi daban -daban, da inganta kyakkyawar niyya da karfafa alaka.

Janar Ahmed ya bayyana cewa rabon tallafin ya kai kimanin yara marayu da mabukata 400, tare da bayar da littattafan karatun da rubutu da kuma alkalami ga dalibai a fadin makarantun Firamare da Sakandare goma sha daya da ke garin Gusau.

Har ilayau Ya yi nuni da cewa, a yayin da Sojoji ke tallafa wa yankunan karkara, wannan taron ya mayar da hankali ne wajen raba muhimman kayayyaki ga kananan yara, marayu da kuma marasa galihu a garin na Gusau, Inji shi.

Kwamandan Birgade dai yayi amfani da wannan damar wajen yin kira ga al’umma da su hana masu ba da labari ko taimakon ‘yan fashi ta hanyar kai rahoton ayyukansu ga soji. Maimakon haka, ya ja hankalin wadannan ’yan uwa da su tuba su mika makamansu domin dawo da zaman lafiya a jihar da ma sauran jahohin kasar nan, Inji shi.

Kazalika ya bayyana damuwarsa kan ayyukan ‘yan bindiga a jihar, inda ya tabbatar da cewa sojoji suna aiki tukuru don ganin manoma sun yi noma da girbin amfanin gona yadda ya kamata, ta yadda za a tabbatar da samar da abinci da bunkasa tattalin arziki. Ya kuma nemi goyon bayan jama’a da hadin kai ta hanyar baiwa rundunar Sojoji muhimman bayanai domin dawo da zaman lafiya.

Tun da farko, an raba kayayyakin kiwon lafiya ga kananan hukumomi goma sha hudu da ke cikin yankin na Birgediya, an kuma raba littattafan karatun da rubutu na musamman ga daliban firamare, kananan da manyan makarantun sakandare a makarantu goma sha daya da ke Gusau.

Makarantun da suka ci gajiyar wannan karimcin sun hada da Makarantar Firamare ta Nizzamiya, Sabon Garin Gusau, Makarantar Marayu, Karamar firamarai da ke GRA, Gusau, Dan Turai Model Primary School, Hayin Dan Hausa, Sambo sakandare, Tudun Wada, Gusau.

Sauran sun hada da Government Day Secondary School, Unguwan-gwaza Gusau, Government Girls Day Secondary School, Tudun Wada Gusau, General Abdusalam Abubakar Primary School da Kuma wasu gidaje gudu ɗari a cikin garin Gusau, Girls Focal Primary School da Ungwan Zabarma Gusau da Sarkin Kudu Secondary Government Secondary da Government Girls Arabic Secondary School Gusau da NAOWA Creche Nursery and Primary School da kuma Alasawa Gusau.

Wadanda suka ci gajiyar tallafin sun bayyana jin dadin su ga rundunar sojin Nijeriya bisa irin wannan tallafi da aka ba su tare da gudanar da addu’o’i da sakon fatan alheri ga rundanar sojojin ta Nijeriya da kuma gwamnatin jihar Zamfara kan bayar da tallafin.

People are also reading