Home Back

Sojoji Sun Dakile Yunkurin Sake Jefa Arewa a Duhu, Sun Raunata ’Yan Ta’adda

legit.ng 2024/7/23
  • Ba a dade da gyara wutar yankin Arewa maso Gabas ba, 'yan Boko Haram sun yi kokarin kai hari tare da sake lalata wutar
  • Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar dakile harin da maharan suka shirya kan manyan karfunan wutar lantarki
  • Lamarin ya faru ne a kauyen Kesesa da ke bayan garin Damaturu a jihar Yobe a jiya Asabar 6 ga watan Yulin 2024

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Yobe - Rundunar sojojin Najeriya ta yi nasarar dakile harin Boko Haram kan karfunan wutar lantarki.

Dakarun sojojin sun yi nasaarar dakile harin ne a Damaturu da ke jihar Yobe tare da taimakon mafarauta.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Zagazola Makama ya fitar a yau Lahadi 7 ga watan Yulin 2024.

Ya ce lamarin ya faru ne a kauyen Kasesa da ke bayan garin Damaturu inda suka yi kokarin lalata karfunan wutar lantarki.

"Dakarun sojoji sun dakile harin Boko Haram kan manya-manyan karfunan da ke dauke da wutar lantarki a Kasesa da ke bayan garin Damaturu."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Dakarun sun samu nasarar dakile harin ne a jiya Asabar 6 ga watan Yulin 2024 bayan samun bayanan sirri."
"Yan ta'addan sun yi kokarin lalata karfunan wutar kafin dakarun da taimakon mafarauta suka yi nasarar dakile shirin."
"Bayan kai ruwa rana da dakaraun, maharan sun gudu sun bar motarsu da fasassun tayoyi biyu har ma da jini a jikinta da ke nuna sun samu raunuka."

- Zagazola Makama

Rahoton ya ce bayan bincike an gano abubuwan fashewa a motar wacce aka samu wasu katuna mallakin Emmanuel Adamu.

Wutar lantarki ta lalace a Najeriya

Kun ji cewa a jiya Asabar 6 ga watan Yulin 2024 aka sanar da lalacewar wuta a Najeriya kafin daga bisani a yi gaggawar gyarawa.

Wannan na zuwa ne makwanni kadan bayan gyara wutar lantarki a yankin Arewa maso Gabas bayan lalacewarta na tsawon lokaci.

Asali: Legit.ng

People are also reading