Home Back

Kotu Ta Dakatar da Gwamna Kan Binciken Gwamnatin da Ta Shude Daga 2015 Zuwa 2023

legit.ng 2024/9/29
  • Babbar kotun jiha da ke birnin Makurdi a jihar Benue ta dakile shirin binciken tsohon gwamna, Samuel Ortom
  • Kotun ta bukaci Gwamna Alia Hyacinth ya dakatar da binciken har sai kotu ta dauki mataki kan korafin da tsohon gwamnan ya shigar
  • Wannan na zuwa ne bayan kafa kwamitin bincike da Alia ya yi domin bincike daga shekarar 2015 zuwa 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Benue - Babbar kotun jiha a Makurdi ta dakatar da Gwamna Alia Hyacinth binciken tsohon gwmanan jihar, Samuel Ortom.

Kotun ta dauki wannan matakin ne a jiya Laraba 29 ga watan Mayu inda ta ce kwamitin da aka kafa ya dakatar da binciken.

Kotu ta yi hukunci kan binciken tsohon gwamna da Alia ya kafa kwamitin kansa
Kotu a jihar Benue ta dakatar da Gwamna Alia kan binciken Samuel Ortom. Hoto: @SamuelOrtom_/@benuestategovt. Asali: Twitter

Benue: Matakin kotu kan binciken Ortom

Har ila yau, kotun ta ce dakatarwar ya zama dole saboda jiran hukuncin da za a yi bayan shigar da korafi da Samuel Ortom ya yi kan bincikensa, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A watan Fabrairu ne Gwamna Alia ya kafa kwamiti guda biyu domin kaddamar da bincike daga shekarar 2015 zuwa 2023 lokacin mulkin Ortom.

Kwamitocin da gwamnan ya kafa za su yi duba ne ga kudin da aka samu da wanda aka kashe tsawon wa'adin mulkin Ortom, cewar Daily Post.

Mai Shari'a, T. T Asua shi ya dakatar da binciken bayan lauyan Ortom, Oba Maduabuchi ya shigar da korafi kan lamarin.

Lauyan Ortom ya shigar da korafi

Maduabuchi ya ce odita-janar na gwamnatin jihar ya riga ya yi bincike da tabbatar da asusun gwamnatin babu matsala.

Ya ce bayan kammala bincike oditan ya mika rahoton bincikensa ga Majalisar jihar kamar yadda tsarin doka ya tanadar.

Har ila yau, lauyan ya ce duba da tarin hujjoji da ya zayyano bai kamata a ci gaba da tuhumar Ortom ba.

Alia ya gargadi tsofaffin gwamnoni a jiharsa

Kun ji cewa Gwamna Alia Hyacinth ya gargadi tsofaffin gwamnoni jihar da su bar shi ya ci gaba da ayyukan alheri da ya fara.

Alia ya ce idan har wani tsohon gwamnan ba zai kawo shawara da za ta kawo ci gaba a jihar ba ya ja bakinsa ya yi shiru.

Asali: Legit.ng

People are also reading