Home Back

Me ya sa ba ku so a ɓambare kananan hukumomi daga ƙarƙashin ku – Kotun Koli ga Gwamnoni

premiumtimesng.com 2024/7/6
MATSALAR TSARO: Bayan dawowa daga taron Amurka, gwamnonin Arewa sun tattauna matsalolin tsaro a Kaduna

Kotun Ƙoli ta umarci gwamnonin Najeriya 36 kowa ya aika da bayanan kare kai daga ƙarar da Antoni Janar na Tarayya, Lateef Fagbemi ya shigar, inda ya nemi kotun ta bai wa ƙananan hukumomin Najeriya ‘yancin cin gashin kan su da mallakar da gwamnonin jihohi suka yi masu.

Alƙalan Kotun Ƙoli bakwai ne suka zartas da umarnin a ranar Alhamis ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Lawal Garba.

Kotun ta ce su kai bayanan kare kan su a cikin kwanaki biyar.

A ranar Alhamis ɗin ce dai aka fara zaman shari’ar.

Wannan jarida ta buga labarin cewa Gwamnatin Tarayya ta maka gwamnoni 36 Kotun Ƙoli, ta na so a bai wa ƙananan hukumomi cin gashin kan su.

Gwamnatin Tarayya ta maka gwamnonin Najeriya 36, inda ta ke roƙon kotu ta tirsasa ƙwatar wa ƙananan hukumomin ƙasar nan 774 cin gashin kan su, wato a riƙa ba su kuɗaɗen su kai-tsaye, ba tare da an bai wa jihohi su ba su ba.

Ofishin Antoni Janar kuma Ministan Harkokin Shari’a na Tarayya ne ya shigar da ƙarar a Kotun Ƙoli, ya na neman kotun ta bai wa ƙananan hukumomin cin gashin kan su.

A cikin ƙara mai lamba SC/CV/343/2024, gwamnatin tarayya na so Kotun Ƙoli ta haramta wa gwamnoni rushe zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi.

Haka kuma ta na so a riƙa tura wa kowace ƙaramar hukuma kuɗaɗen ta kai-tsaye, ba ta hannun gwnonin jiha na.

Antoni Janar kuma Ministan Shari’a Lateef Fagbemi na kuma so Kotun Ƙoli ta haramta wa gwamnoni naɗa shugabannin riƙon ƙananan hukumomi.

An dai shirya za a saurari ƙarar a ranar 30 ga Mayu.

An daɗe ana ƙorafin yadda gwamnonin jihohi ke sarrafa ƙananan hukumomi.

Ko kwanan nan tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, Farfesa Attahiru Jega ya ce zaɓen shugabanni ba shi da bambanci da taron naɗa basaraken gargajiya.

People are also reading