Home Back

KANO: Duk da kisisina, makirci, bita-da-kulli, zagon kasa da ake yi wa gwamna Yusuf, ya taka rawar gani a shekararsa ta farko – Kwankwaso

premiumtimesng.com 2024/6/30
KANO: Duk da kisisina, makirci, bita-da-kulli, zagon kasa da ake yi wa gwamna Yusuf, ya taka rawar gani a shekararsa ta farko  – Kwankwaso

Shugaban Kwankwasiyya kuma ubangidan gwamnan Kano Abba Yusuf, Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa mahassada, ƴan bakin ciki da ƴan zagon kasa ne suka saka gwamnatin Abba Yusuf a gaba ya sa bai iya kaiwa ga duka abubuwan da ya yi niyyar yi ba cikin shekara ɗaya.

Sai dai kuma kwankwaso ya ce duk da haka gwamna Yusuf ya taka rawar gani a jihar Kano.

” Tun da aka rantsar da gwamna Yusuf gwamnan Kano ya fara fuskantar ƙalubale daga abokan adawa. Sun ki su saki, muka je kotu da su, Allah ya bamu sa’a a.

” Bayan haka kuma su rika bullo mana da maƙirci dabandaban, ta yau da ban da irin ta gobe. Bita da ƙulli, da kisisina babu wanda ba a kulla wa gwamnatin ba amma duk da haka cikin shekara ɗaya gwamna Yusufta yi abin azo a gani.

Kwankwaso ya ce irin haka shima aka yi masa lokacin da ya dawo karo ta biyu.

” Nima haka aka rika yi min lokacin da na dawo karo na biyu. Muka fara samun tashin bamabamai, a masallatai, Kasuwanni da asibitoci duk don a kawo mana cikas amma duk da haka muka yi nasara.

A jawabin sa, gwamnan Yusuf ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta gyara makarantu firamare da na sakandare a kananan hukumomin jihar kaf.

People are also reading