Home Back

Faransa ta mara wa shirin fara sarrafa rigakafi a Afirka

dw.com 2024/7/2
Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron

Gwamnatin kasar ta Faransa dai ta za ta dafa wa shirin da zai lakume dala biliyan guda na Amurka, bayan gibi da ak gani wajen samun alluran rigakafi a lokacin da duniya ke kokarin yaki da annobnar Corona a baya.

Shugabannin kasashen Afirka da dama da sauran kungiyoyin fafutika sun yi zargin rashin yi wa Afirka adalci wajen samar da magugunan rigakafin lokacin da duniya ta tasan ma yaki da Coronar a 2020.

Yanzu dai Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai da sauran kungiyoyin duniya ne suka shirya taimaka wa nahiyar ta Afirka domin iya tinkarar duk wata annoba a nan gaba.

People are also reading