Home Back

A Karon Farko, Sanusi II Yayi Magana a Kan Rikicin Sarautar Kano da Aminu Ado Bayero

legit.ng 2024/7/4
  • Muhammadu Sanusi II ya yi magana da manema labarai a wata hira, ya tabo zancen sabanin da aka samu a masarauta
  • Basaraken ya zargi gwamnatin Kano da raba kan gidan dabo, inda aka nada Aminu Ado Bayero bayan an cire masa rawani
  • Sanusi II ya ce dawo da shi kan karaga da rusa kirkirarrun masarautu ya dawo da kima da martabar Sarkin Kano a tarihi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Kano - Muhammadu Sanusi II ya yi magana kan rigimar da ta shigo masarautar Kano bayan an sauke sarakunan da aka kirkiro a 2020.

A watan da ya gabata gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sa hannu a sabuwar dokar da ta tsige Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna.

Sanusi II da Aminu Bayero
Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero na ikirarin sarautar Kano Hoto: @SanusiSnippets, #HRHBayero Asali: Twitter

Muhammadu Sanusi II ya yi hira da jaridar Sun, inda ya bayyana cewa wadanda aka nada bayan sauke shi a 2020 suna jin haushin tsige su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai martaba bai ambaci Sarki Aminu Ado Bayero ba, amma kalamansa suna nuni gare shi ne domin shi aka tsige domin maida shi.

Mu na cikin wani yanayi da wani ya raba mu. Kuma idan aka kawo irin wadannan abubuwa, wasu za su samu wasu damammaki.

Ba su nema ba, amma sun ci moriyarsa na shekaru hudu.

Yanzu kuma da suka rasa, ya zama matsala. Amma ba yau aka samu matsalar ba. Tun shekaru hudu da suka wuce, aka haifar da ita,

Da tun farko ba ayi wannan ba, da ba a kai ga haka a yau ba. Dangi daya ne, mutane guda. Wani ya zo ya rabu.

Daily Trust ta rahoto Sanusi II yana kuka kan yadda aka kacalcala masarautar Kano, aka kirkiro wasu, abin da ba ayi a shekaru 1000 ba.

Ko a cikin gidan, ya dauki masarauta guda ya ba wani gida. Yanzu da aka karbe daga hannunsu bayan shekaru hudu, ya zama matsala.

Sarkin ya ce ba kowa ake hari ba, gwamna ya ga bukatar dawo da kimar masarautar ne, sai dai hakan zai yi wadanda aka sauke ciwo.

Asali: Legit.ng

People are also reading