Home Back

Sanusi II Vs Aminu: Babbar Kotu Za Ta Yanke Hukunci a Shari'ar Sarautar Kano

legit.ng 2024/7/3
  • Babbar kotun tarayya za ta yanke hukunci kan ko tana da hurumin sauraron shari'ar sarautar Kano yau Alhamis, 13 ga watan Yuni
  • Aminu Babba Ɗanagundi ne ya kai ƙara gaban kotun yana ƙalubalantar matakin gwamnatin Kano na mayar da Sarki Sanusi II
  • A zaman shari'ar, lauyoyi sun gwabza kan hurumin kottun wanda a ƙarshe aka tsara yanke hukunci yau Alhamis

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - A yau Alhamis, 13 ga watan Yuni, babbar kotun tarayya mai zama a Kano za ta yanke hukunci kan ko tana da hurumin sauraron kara kan rigimar sarautar Kano.

Idan baku manta ba gwamnatin Kano karkashin jagoancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta mayar da Muhammadu Sanusi kan sarauta a matsayin sarki na 16.

Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero.
Yau kotun tarayya za ta sanar da hukuncinta kan hurumin sauraron shari'ar sarautar Kano Hoto: @ImranMuhdz Asali: Twitter

Rahoton Leadership ya ce Aminu Babba Danagundi, daya daga cikin dattawan masarautar Kano da aka tube ya maka gwamnatin Kano a gaban kotun yana neman haƙƙinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗanagundi ya roƙi kotun ta dawo masa da haƙƙinsa wanda yake zargin gwamnatin Kano ta take a lokacin da ta tsige shi daga sarautar Sarkin Dawaki Babba.

Lauyoyin wadanda ake kara sun yi muhawara sosai kan hurumin kotun tarayya a batun da ya shafi dokar da ta tsige Aminu Bayero a matsayin Sarkin Kano na 14.

Barista M. A. Waziri, lauyan wanda ya shigar da kara, Aminu Danagundi, wanda aka tsige daga Sarkin Dawaki Babba, ya cw kotu na da cikakken hurumin sauraren karar.

Ya kuma kara da cewa ba a yi wa wanda yake karewa adalci ba kafin a tsige shi, don haka an tauye masa hakki, kuma tsarin da aka bi na dawo da Sarki Sanusi II ya saɓa doka.

A ɗaya bangaren, lauyan Sanusi II, Barista Muhamud A. Magaji, ya bukaci kotun da ta yi watsi da duk bayanin mai kara na cewa tana da hurumin ci gaba da shari’ar.

Ya kara da cewa babu shakka majalisar dokokin jihar tana da hurumin gyara, soke ko ma samar da wata doka da ta dace da jihar.

A ƙarshe dai kotun ta ɗage zaman zuwa yau Alhamis domin yanke hukunci kan ko tana da hurumin sauraron shari'ar rikicin sarautar da ke faruwa a Kano.

Asali: Legit.ng

People are also reading