Home Back

Sudan ta zargi UAE da rura wutar rikicin yakin basasar kasar

dw.com 2024/7/6
Hoto: AFP

Gwamnatin mulkin sojin Sudan ta zargi Hadaddiyar Daular Larabawa da rura wutar rikicin yakin basasar kasar da aka shafe watanni 14 ana gwabzawa, ta hanyar tallafawa dakarun RSF na Mohamed Hamdan Dagalo da makamai.

Jakadan Sudan a Majalisar Dinkin Duniya Al-Harith Mohamed ne ya yi wannan zargi, yayin taron kwamitin tsaro na majalisar, yana mai cewar ikirarin mika korafin kasar gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, kan rawar da Hadaddiyar Daular Larabawan ke takawa a yakin.

Tuni dai Hadaddiyar Daular Larabawan ta yi watsi da wannan zargi, inda ta bayyana kalaman a matsayin abin kunya marar tushe balle makama, in ji jakadanta a Majalisar Dinkin Duniya Mohamed Abushahab.

Sudan din dai ta ce tana da hujjojin da suka nuna karara cewa dakarun RSF na far wa fararen hula da makaman da suka karba daga Hadaddiyar Daular Larabawa.

People are also reading