Home Back

IFAD Da Gwamnatin Tarayya Sun Yi Hadaka Don Bunkasa Aikin Noma A Arewa

leadership.ng 2024/5/2
IFAD

Gidauniyar Bunkasa Aikin Noma ta Kasa da Kasa (IFAD), tare da hadakar gwamnatn tarayya, za su fitar da wani sabon aiki na habaka aikin noma, wanda Manoman Arewacin kasar nan ke yi; domin samun riba (BCN).

Wasu kwararru, a yayin wani taron bita da aka gudanar a kan aikin na (BCN) sun bayyana cewa, sabon aikin zai taimaka wajen kara bunkasa aikin noma, domin samun riba tare da kara habaka noman da manoman yankin na Arewa ke yi.

Haka zalika, a makon da ya gabata ne, Mataimakin Shugaban gidauniyar ta IFAD, Dakta Donal Brown; a wani taron manema labarai a lokacin wata ziyara da ya kawo Nijeriya ya bayyana cewa, wannan sabon aikin zai matukar taimaka wa manoman da ke Arewacin Nijeriya, musamman a kan yadda za su kara samun wasu daga cikin damammaki a wannan fani na aikin noma.

A cewar tasa, “Tare da hadin guiwar gwamnatin tarayya ne, muka tsara wannan aikin, domin mara wa manoman da ke yankunan Arewacin wannan kasa goyon baya, wajen bunkasa nomansu tare da kuma jure wa kowane irin sauyin yanayi”.

Dakta Donal ya ci gaba da cewa, “Ko shakka babu, an yi matukar samun cin nasara a wannan aiki a Nijeriya, inda ya kara da cewa, ayyukan jin kai na BCDP, na matukar inganta rayuwar iyalai na (LIFE-ND), ta hanyar wannan sabon aikin kuma za a samu cin nasara tare da kuma sauran ayyukan”.

Tun a shekarar 1978, wannan gidauniya ta IFAD ta kashe kimanin dala biliyan 1.5 a Nijeriya, haka nan kuma; kudaden da gidauniyar ta kashe a halin yanzu, sun kai kimanin dalar Amurka miliyan 400.

People are also reading