Home Back

Kotu ta umarci lauyoyi su rubuto Martanin su a kan shari’ar rushe masarautun Kano

dalafmkano.com 2024/7/4

Babbar kotun tarayya mai zamanta a Gyadi-gyadi a Kano, karkashin mai Shari’a Abdullahi Muhammad Liman, ta ɗage zaman da ta fara na sauraron shari’ar da Aminu Babba Dan agundi ya shigar yana kalubalantar gwamnatin jahar jano akan batun kwaskwarimar da majalisar dokokin jahar kano tayi wa dokar masarautu a jihar nan.

A zaman kotun na yau lauyan wadanda akayi kara barrister Mahamud Abubakar Magaji ya bayyanawa kotun cewar, a zaman yau za a tattauna ne kawai akan batun hurumin kotun akan wannan sharia sai dai lauyan mai kara batister waziri ya shaidawa kotun cewar basu rubuta martaninsu akan wannan batu ba, a nan kotun ta umarce su da su rubuto martaninsu nan da awa daya.

Tun da fari dai Aminu Babba Dan agundi ne ya shigar da shari’ar yana karar gwamnatin kano da majalisar dokoki, sakamakon gyaran fuska da majalisar tayi wa dokar masarautun jahar kano ta 2019, wadda ta rushe masarautu 4 da aka kirkira kuma daga bisani gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu, tare da bayyana Mallam Muhammadu Sunusi na biyu a matsayin sarkin Kano na 16.

Wakilinmu na Kotu Yusuf Nadabo Isma’ila ya rawaito cewa, yayin zaman an girke jami’an tsaron ƴan sanda da na DSS, wanda suka hana shiga harabar babbar kotun tarayya da ke Kano, da ta saurari shari’ar da Aminu Babba Ɗan Agundi, ya shigar yana ƙalubalantar rushe masarautun Kano.

Jami’an tsaron sun kuma hana kowa shiga harabar kotun, sai iya wadanda suke da hurumi a Shari’ar, da ƴan Jarida, wanda ake sa ran fara sauraron ƙarar nan bada jimawa ba.

People are also reading