Home Back

Atletico ta ki sallama tayin da Chelsea ta yi wa Omorodion

bbc.com 2024/7/6
Samu Omorodion

Asalin hoton, Getty Images

Chelsea ta tattauna da dan kwallon Atletico Madrid, mai shekara 20 dan kasar Sifaniya, Samu Omorodion.

Tuni Atletico Madrid ta hana Chelsea ci gaba da tuntubar dan kwallon, bayan da ta ki sallama tayin £34m da kungiyar Stamford Bridge ta yi har da karin tsarabe-tsarabe.

Omorodion ya nuna kansa a kakar da ta wuce, wanda ya ci kwallo tara a wasannin aro karo 35 da ya buga wa Deportivo Alaves.

Chelsea na shirin yin zawarcin masu cin kwallaye kan fara kakar bana, ciki har da matashin Aston Villa, mai shekara 20, Jhon Duran.

Kungiyar Stamford Bridge ta tsara bayar da kudi ga dan wasan tawagar Colombia, sannan ta yi musaya da matashinta mai shekara 22 Ian Maatsen ga Villa.

Haka kuma Chelsea na sa ran tuntubar dan wasan Stuttgard, mai shekara 28, Serhou Guirassy, wanda yake da kunshin yarjejeniyar £15m da aka sabunta a bana.

Ita kuwa Crystal Palace ta bai wa Chelsea damar tuntubar Michael Olise, mai shekara 22, wanda Newcastle United da Bayern Munich ke shirin yin zawarci.

Olise yana da kunshin kwantiragin £60m kuma mai sarkakiya da za a bayar da wani kaso ga tsohuwar kungiyarsa, Reading da Palace da shi kansa, Olise.

Tuni Chelsea ta kammala daukar mai tsaron bayan tawagar Ingila, Tosin Adarabioyo, mai shekara 26 daga Fulham.

Sannan tana daf da kammala cinikin £29m kan mai shekara 17 mai taka leda a Palmeiras, Estevao Willian – amma sai a kakar badi zai koma Stamford Bridge lokacin ya cika shekara 18 da haihuwa.

People are also reading