Home Back

Arsenal Ta Sake Tabbatar Da Cancantar Lashe Firimiya

leadership.ng 2024/5/14
Arsenal Ta Sake Tabbatar Da Cancantar Lashe Firimiya

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta yi raga-raga da Chelsea a kwantan wasan Prem-ier League da suka buga ranar Talata a Emirates bayan ta zura kwallaye biyar rigis a ragar Chelsea.

Minti hudu da fara wasa Arsenal ta zura kwallo a ragar Chelsea ta hannun Leandro Trossard, kuma haka suka je hutun rabin lokaci sai dai Arsenal ta buga kwallo zuwa raga sau 13 tun kan hutu, karo na farko da ta yi wannan kwazon a wasa da Chelsea a Premier League, tun bayan 2003 zuwa 2004.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Arsenal ta kara kwallo ta biyu ta hannun dan wasa Ben White, sannan Kai Habertz ya ci biyu a fafatawar ta hamayya, a karo na far-ko da ya taba zura kwallaye biyu a wasa daya.

Dan wasa Kai Habert ya zama na farko da ya ci Chelsea kwallo biyu a Premier League, bayan da ya buga wa kungiyar wasa a baya kafin ya koma Arsenal a farkon wannan kakar.

Wannan shi ne karon farko da Arsenal ta zura 5-0 a ragar Chelsea a gida a babbar gasar Firimiya ta Ingila, tun bayan 5-2 da ta yi nasara ranar 16 ga watan Afirilun 1979 lokacin rukunin farko

Chelsea ta fara karawar da ‘yan wasa masu matsakaicin shekara kasa da 24, kuma a karo na bakwai da ta yi hakan a Premier League a bana, sai dai kungiyar Leeds United ce kan gaba a irin wannan kokarin a 1999 zuwa 2000, wadda ta yi hakan karo 10.

Da wannan sakamakon Arsenal tana ta daya a kan teburi da maki 77, sai Liberpool ta biyu da maki 77 da kuma Manchester City mai maki 77 mai kwantan wasa guda daya.

Chelsea kuma tana ta taran teburi da maki 47 da tazarar maki daya tsakani da West Ham ta takwas da tazarar maki uku tsakani da Manchester United ta bakwai da New-castle United ta shida masu maki 50 kowacce.

People are also reading