Home Back

Nazarin sabon albashin jami'an gwamnatin Kenya

dw.com 4 days ago
Amfani da karfi kan masu zanga-zanga a Kenya
Amfani da karfi kan masu zanga-zanga a Kenya

A wannan Laraba fadar shugaban kasar Kenya ta ba da umurnin sake nazari kan karin albashin da aka yi wa masu rike da mukaman gwamnati, a wani matakin na rage zaman tankiya a kasar sakamakon zanga-zangar da aka fuskanta ta nuna kiyayya ga gwamnati, saboda yunkurin kara haraji na kayan da mutane suke amfani da su na yau da gobe.

Matasan kasar ta Kenya sun fadada bukatar neman ganin Shugaba William Ruto ya ajiye aiki saboda yadda gwamnatinsa ta gaza magance matsalar cin hanci da rashawa gami da bushasha da dukiyar kasa. Gwamnatin Kenya tana shan suka daga kungiyoyin kare hakkin dan Adam bisa amfani da karfi kan masu zanga-zanga inda kimanin mutane 30 suka halaka lokacin zanga-zangar sannan an kama wasu kimanin 270.

People are also reading