Home Back

Atiku ya bayyana matsayarsa kan takarar shugaban kasa a zaben 2027, an yaɗa bidiyon

legit.ng 2024/9/29
  • Ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar ya magantu kan tsayawa takara a 2027
  • Atiku ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a zaben 2027 a cikin wani faifan bidiyo a yau Laraba 22 fa watan Mayu
  • Hakan ya biyo bayan wata ganawa da ya yi da ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter Obi a kwanakin baya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a 2027.

Atiku ya tabbatar da haka ne a yau Laraba 22 ga watan Mayu yayin hira da 'yan jaridu..

Ɗan takarar shugaban kasar ya bayyana haka kwanaki kadan bayan ganawa da takwaransa na LP, Peter Obi.

Jigon PDP, Abdul'aziz Na'ibi Abubakar ya tabbatar da haka a shafinsa na X tare da faifan bidiyo.

Sai dai Atiku bai bayyana wanda zai yi masa mataimaki ba a zaben 2027 yayin hirar da ya gabatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Abin farin ciki ga duk ƴan Najeriya yayin da Atiku Abubakar ya tabbatar zai tsaya takara a zaben 2027."
"Shin kun shirya zabensa a 2027?"

- Abdul'aziz Na'ibi Abubakar

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

People are also reading