Home Back

"Ku Daina Biyan Kudin Fansa": Sanata Ya Ba 'Yan Najeriya Mafita Kan Rashin Tsaro

legit.ng 2024/7/2
  • Sanata Abdul'aziz Musa Yar'adua ya buƙaci ƴan Najeriya da su daina biyan kuɗaɗen fansa idan aka sace ƴan uwansu
  • Sanatan ya yi nuni da buƙatar da ke akwai ta barin gwamnati ta shawo kan matsalar maimakon ba ƴan bindiga kuɗaɗen fansa
  • Ya bayyana cewa biyan kuɗaɗen fansa ga ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane bai yin komai face ƙara musu ƙarfin aikata ta'addanci

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Sanata Abdulaziz Musa Yar’adua ya buƙaci ƴan Najeriya da su daina biyan kuɗaden fansa ga masu garkuwa da mutane da ƴan bindiga.

Sanatan ya bayyana cewa biyan kuɗaɗen fansan ba komai yake yi ba face ƙara ƙarfin ƴan bindigan wajen aikata ta'addanci.

Sanata ya bukaci a daina biyan kudin fansa
Sanata Abdul'aziz Yar'adua ya bukaci a daina biyan kudin fansa Hoto: Abdul'aziz Musa Yar'adua Asali: Facebook

Sanatan mai wakiltar Katsina ta Tsakiya ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a shirinsu na 'Sunrise Daily' a ranar Juma'a, 7 ga watan Yunin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Abdul'aziz Yar’adua, shi ne shugaban kwamitin majalisar dattawa kan sojoji.

Illar biyan kuɗaɗen fansa ga ƴan bindiga

Sanatan ya nuna cewa duk da tsoro da firgicin da mutane ke shiga idan aka sace ƴan uwansu, ya kamata mutane su amince cewa gwamnati za ta iya shawo kan matsalar.

Ya bayyana cewa biyan kuɗaɗen fansan ba komai yake yi ba face ƙarawa ƴan bindigan ƙarfin ci gaba da munanan ayyukansu.

"Ya kamata mutane su sani cewa batun tsaro abu ne wanda ya shafi kowa. Saboda haka ya zama wajibi a ba gwamnati damar jagorantar fuskantar matsalar."
"Bai kamata wasu tsiraru su ɗora wannan nauyin a kansu ba. Saboda da zarar an ba su kuɗin fansa kamar an ƙara musu ƙarfin ci gaba da ta'addanci ne."
"Saboda waɗannan kuɗaɗen da su suke amfani wajen siyan makamai da sauran kayayyakin aikata ta'addanci."
"Yana da kyau ƴan Najeriya su fahimci buƙatar da ke akwai ta su daina biyan kuɗaɗen fansa idan aka sace ƴan uwansu."

- Sanata Abdul'aziz Musa Yar'adua

Sanata Abdul'aziz ya kare Lagbaja

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Abdul'aziz Yar'adua ya yi martani game da harin bam kan masu Maulidi a jihar Kaduna.

Yar'adua ya ce wannan harin an samu kuskure ne wanda ba ya bukatar sai hafsan sojoji, Manjo Janar Taoreed Lagbaja ya yi murabus.

Asali: Legit.ng

People are also reading