Home Back

Binance Ya Sake Samun Matsala Bayan an Lafta Masa Tara Mai Yawa

legit.ng 2024/7/3
  • Mahukunta a ƙasar India sun ci tarar babban kamfanin hada-hadar kirifto na duniya bisa zargin keta dokokin ƙasar
  • Hukumar FIU ta ci tarar Dala miliyan 2.25 kan kamfananin na Binance bayan ta same shi da keta dokar hana safarar kuɗaɗe ta ƙasae da ke nahiyar Asia
  • Tarar na zuwa ne yayin da kamfanin ke fuskantar tuhumomi a Najeriya kan zargin safarar kuɗaɗen haram da ƙin biyan haraji

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ƙasar India - Hukumar FIU ta ƙasar India ta ci tarar Dala miliyan 2.25 (Rupee miliyan 188.2) kan Binance, babban kamfanin hada-hadar kirifto ta duniya.

Hukumar FIU ta ci wannan tarar ne kan Binance saboda yin aiki a ƙasar ba tare da yin rajista da hukumar ba, kamar yadda doka ta tanada.

An ci Binance tara a India
Hukumomi sun ci kamfanin Binance tarar $2.25m a India Hoto: @_RichardTeng, @binance Asali: Twitter

Hukumar ta FIU ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da jaridar The Punch ta samu daga shafinta na yanar gizo ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane laifi Binance ya yi a India?

Hukumar ta ce Binance, a matsayin mai rajista a ƙasar, ya keta sassa uku na dokar hana safarar kuɗaɗe ta ƙasar ta shekarar 2002, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.

Wannan dai ita ce matsala ta baya-bayan nan da ta tunkaro Binance, wanda ke fuskantar shari'a a Najeriya kan badaƙalar kuɗaɗen haram da kuma zargin ƙin biyan haraji.

A Najeriya, hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta zargi Binance da karkatar da sama da Dala miliyan 35.

Har ila yau dai Binance na fuskantar wata shari’a ta daban kan kaucewa biyan haraji da hukumar tara haraji ta ƙasa ta shigar.

Binance ya gaza cika sharuɗɗa a India

Binance ta yi rajista tare da hukumar FIU a watan Mayu, domin neman ci gaba da aiki a India bayan da aka buƙaci ya yi hakan a watan Disamban 2023.

Duk da haka, kamfanin ya gaza bin ƙa'idodin, wanda ya kai ga cinsa tara mai yawa.

An nemi cin hanci a hannun Binance

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kamfanin Binance, Richard Teng, ya yi iƙirarin cewa wasu mutanen da ba a san su ba sun nemi cin hancin kirifto daga hannun jami'an kamfanin.

Shugaban na Binance ya ce an nemi cin hancin ne a hannun Tigran Gambaryan da Nadeem Anjarwalla, kafin a tsare su a ranar 28 ga Fabrairun 2024.

Asali: Legit.ng

People are also reading