Home Back

'Yan Bindiga Sun Yiwa Jami'an Tsaro Kwantan Ɓauna, An Rasa Rayuka a Katsina

legit.ng 3 days ago

Jihar Katsina - 'Yan bindiga sun kashe jami’an ‘yan sanda biyar a wani harin kwantan bauna da suka kai a karamar hukumar Jibia da ke jihar Katsina.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Mazauna yankin sun ce lamarin ya faru ne da safiyar Lahadi a yayin da ƴan sandan ke hanyar zuwa cikin garin Jibia daga sansaninsu da ke kauyen Zandam.

Sufetan ƴan sanda, IGP Kayode.
Yan bindiga sun kashe yan sanda 5 a Jibia da ke Katsina Hoto: PoliceNG Asali: Twitter

Jaridar Premium Times ta tattaro cewa ƴan sanda huɗu sun mutu ne nan take a wurin yayin da ɗan sanda ɗaya ya ƙarisa a asibitin FMC da ke Katsina.

Bayanai sun nuna cewa ƴan ta'addan sun sace bindigun AK47 guda biyat bayan sun kashe jami'an tsaron da misalin ƙarfe 6:00 na safiyar ranar Lahadi.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Aliyu ya ce zai yi magana nan ba da jimawa ba idan ya gama tattara bayanai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton bai fitar da wani ƙarin bayani ba amma wani rahoton tsaro ya tabbatar da faruwar lamarin.

Rahoton tsaro ya bayyana wurin da aka kai harin a matsayin wuri mai hadarin gaske kuma ya gargadi jami’an ‘yan sanda su gujewa bin wannna titin.

Ƴan bindiga dai na yawan kai hare-hare a yankin ƙaramar hukumar Jibia ta jihar Katsina da kuma garuruwan da ke makwaftaka da jihohin Zamfara da Kaduna.

Asali: Legit.ng

People are also reading