Home Back

Kantomomi, Malamai, da masu riƙe da masarautun gargajiya na Kano ta tsakiya sun yi mubaya’a ga Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu

dalafmkano.com 2024/6/28

Shugabannin riƙo na dukkanin ƙanananan hukumomi 15 na Kano ta tsakiya da dukkanin masu riƙe da masarautun gargajiyar yankin, sun yi mubaya’a ga Sarkin Kano Mallam Muhammadu Sunusi na biyu, tare da nuna goyon bayan su a gare shi.

Shugabannin riƙon na ƙananan hukumomin, da hakimai, da Malamai, da kuma Dagatai, da masu unguwanni, da kuma wasu aga cikin al’ummar yankin na Kano ta tsakiya, sun yi mubaya’ar ne yayin da suka ziyar ci fadar mai martaba sarkin Kano na 16, Mallam Muhammadu Sunusi na biyu, yau Asabar.

Da yake jawabi ga Dala FM Kano, jim kaɗan da yin mubaya’ar, shugaban ƙungiyar shugabannin riƙo na ƙananan hukumomin Kano 44, kuma shugaban ƙaramar hukumar Tarauni Abdullahi Ibrahim Bashi, (Mai Kano) ya ce sun yi mubaya’ar ne bisa yadda mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sunusi, yake da kishin al’umma.

Ya kuma ce baya ga mubaya’ar ƙannanan hukumomin Kano ta tsakiya a yau Asabar, a gobe Lahadi, da ranar Litinin suma ɗaukacin shugabannin ƙananan hukumomin Kano ta Arewa da ta Kudu, da masu riƙe da masarautun gargajiya, da kuma malamai, za su je fadar Sarkin domin yin mubaya’ar.

A nasa jawabin mai martaba sarkin Kano Mallam Muhammadu Sunusi na biyu, ya hori, shugabannin ƙananan hukumomin na Kano ta tsakiya, Malamai, da Hakimai, da Dagatai, da kuma masu unguwannin, da su mayar a hankali wajen samar da ci gaban al’umma.

Wannan dai na zuwa ne bayan da mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu, ya karɓi takardar kama aiki a ranar Juma’a 24 ga watan mayun 2024, bayan da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu a dokar masarautun da majalisar dokokin jihar suka yi wa kwaskwarima, wadda ta rushe sarakuna biyar a jihar Kano, wadda tsohuwar gwamnatin Ganduje ta samar a shekarar 2019.

People are also reading