Home Back

Brighton na son Summerville, Torres baya son barin Barcelona

bbc.com 2024/7/6

Asalin hoton, Getty Images

.
Bayanan hoto, Crysencio Summerville

Brighton ta fara tattaunawa da Leeds kan dan wasan Poland Crysencio Summerville mai shekara 22. (Talksport)

West Ham na son dan wasan Sifaniya Ferran Torres, mai shekara 24, a wannan kakar, sai dai da alama dan wasan baya son barin Barcelona. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Brentford ta yi watsi da kokarin da Tottenham ke yi na dauko dan wasan tsakiya na Ingila Ivan Toney, mai shekara 28. (Football Transfers)

Fenerbahce na son dan wasan Sweden mai taka leda a Manchester United, Victor Lindelof, mai shekara 22. (Sky Germany)

Juventus na son dan wasan Ingila mai taka leda a Mancherster United Jadon Sancho, mai shekara 24, amma saboda farashin fam miliyan 40 da aka yi kan dan wasan, watakila dole kanwar naki ta dauke shi bashi maimakon siyan shi dungurugum. (Sun)

Atletico Madrid na yunkuri kan dan wasa Conor Gallagher mai shekara 24, wanda ke bugawa Ingila wasa da taka leda a Chelsea (Relevo - in Spanish)

Sai dai shi ma Gallagher, din ka iya watsi da komawa Aston Villa, saboda baya muradin taka leda a kulub din. (Football Insider)

Dan wasan Brazilia Estevao Willian, ya kammala gwajin lafiyarsa da Chelsea, wadda ta amince da daukar matashin mai shekara 16 daga kungiyar Palmeiras a watan jiya. (Standard), external

Nottingham Forest na gab da kammala tattaunawa kan mai tsaron ragar Brazil da ke taka leda a Corinthian, wato Carlos Miguel, dan shekara 25, kuma zai kasance mai tsaron ragar da ya fi kowa tsawo cikin 'yan wasan Premier League, tsawon Miguel dai ya kai kafa 6/8. (Daily Mail)

Manchester City ta fara shirye-shiryen shiga zango na gaba ba tare da sayan sabbin 'yan wasa, amma hakan ka iya sauyawa idan wani daga cikin 'yan wasan da ta ke da su ya bukaci komawa wata kungiyar da taka leda. (ESPN)

Newcastle na son dan wasan Iceland, Jon Dagur Thorsteinsson, dan shekara 23, wanda ke taka leda a kulub din OH Leuven na Belgium. (Chronicle Live)

People are also reading