Home Back

EFCC Ta Fallasa Tsohon Gwamna, Tsofafffin Ministocin da Ke Shirya Mata Makarkashiya

legit.ng 2 days ago

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta bayyana masu hannu a zanga-zangar da ake shirin yi domin nuna adawa da ayyukanta.

Hukumar EFCC ta ce wani tsohon gwamna da wasu tsofaffin ministoci biyu ne ke da hannu a zanga-zangar da ake shirin shiryawa.

EFCC ta fadi masu hannu a zanga-zangar da ake shirya mata
EFCC ta fadi masu hannu kan zanga-zangar da ake shiryawa a kanta Hoto: @OfficialEFCC Asali: Facebook

EFCC ta ce duk da zanga-zangar da aka shirya, jami’anta za su ci gaba da gudanar da ayyukansu ba tare da wani shakku ba.

Kakakin hukumar EFCC, Dele Oyewale ne ya bayyana haka a lokacin da yake amsa tambayoyi daga wajen ƴan jarida a yayin wani taron manema labarai a Abuja, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake amsa tambaya kan babban abin da ya janyo zanga-zangar da aka shirya yi, Dele Oyewale ya ce saboda ayyukan hukumar na shafar wasu masu wawurar dukiyar ƙasa ne, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

"Gabaɗaya dukkanin waɗannan mutanen masu maganar a kawo ƙarshen EFCC, kada a kawo ƙarshen EFCC, a ruguza EFCC, kada a ruguza EFCC, mutane ne waɗanda ayyukan hukumar ke shafa."
"Idan akwai hukuma irin EFCC, kuma ba a yi mata irin wannan sukar, hakan na nufin ko dai ba mu yin aikin da ya dace ko jama'a ba su damu da abin da muke yi ba."
"Saboda haka, mun san cewa tabbas ayyukanmu suna shafar mutanen da ba su da gaskiya, kuma muna sane da cewa dole ne za su so su yaƙe mu."

- Dele Oyewale

Asali: Legit.ng

People are also reading