Home Back

Yara fiye da miliyan 240 ke fuskantar tsananin zafi a Asia – UNICEF

dailynews24.ng 2024/5/18

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya ce yara fiye da miliyan 240 ne a yankin Pacific da Gabashin Asiya ke fuskantar tsananin zafin da ba su taba fuskanta ba abin da ake nuna fargaba a kan kamuwa da cutuka da kuma rasa rai. 

Kawo yanzu a shekarar nan, kasashen Thailand da Phillipines da kuma Malaysia sun bayyana cewa zafin da suka fuskanta a bana ba su taba fuskantar irinsa ba. 

Masu hasashen yanayi sun ce za a ci gaba da fuskantar tsananin zafi nan da makonni masu zuwa.UNICEF, ya ce yara ne zafi ya fi yiwa illa fiye da manya.

People are also reading