Home Back

Dattawan Kudancin Kano 103 Sun Buƙaci Gwamna Abba Ya Dawo Da Sarakunan Kano 5 Da Aka Rushe

leadership.ng 2024/7/3
NNPP

A ranar Laraba ne tawagar dattawa 103 daga shiyyar Kano ta Kudu mai wakiltar mazabar Kano ta Kudu da ta hada da Rano, Gaya da Karaye, suka bukaci a maido da masarautu biyar da gwamnatin jihar ta soke don kaucewa wariya da dakile ci gaban da al’ummar yankin suka fara dandana.

Tawagar da ta kunshi tsofaffin kwamishinoni da sauran su, sun zo ne a karkashin jagorancin tsohon kwamishina a Gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau, Musa Salihu Doguwa.

Doguwa ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta yi la’akari da ci gaban zamantakewa da samar da ababen more rayuwa da aka samu bayan kirkiro wadannan masarautu guda biyar da tsohuwar Gwamnatin Abdullahi Ganduje ta yi.

“Mun taru ne a yau domin yin karin haske kan gagarumin ci gaba da inganta sabbin masarautu a kudancin Kano ya kawo a karkashin jagorancin tsohon Gwamna Umar Abdullahi Ganduje.

“Kara darajar Masarautun ya kawo sauyi a fagen faɗaɗa muhimman ababen more rayuwa a al’ummar da ke karkashi da kewayen Masarautar.” in ji Doguwa

People are also reading