Home Back

An Jibge Motocin Jami'an Tsaro Domin Kare Ofishin EFCC Daga Masu Zanga Zanga

legit.ng 3 days ago
  • Jami'an tsaron hadin gwiwa na 'yan sanda da DSS sun fito mota-mota domin bayar da kariga ya ofishin hukumar EFCC da ke Legas
  • Wannan na zuwa ne bayan wasu masu neman a sauya fasalin hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa sun ce za su yi zanga-zanga
  • Hukumar EFCC dai tuni ta zargi wasu tsofaffin gwamnoni da ministoci da ake bincike da daukar nauyin wasu su yi mata tawaye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Legas- An wayi garin Juma'a da ganin tarin jami'an tsaro jibge a ofishin hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC).

An jibge jami'an tsaron a ofishin da ke titin Awolowo a Ikoyin jihar Legas saboda fargabar zanga-zangar kin jinin yadda hukumar ke gudanar da ayyukansu.

Economic and Financial Crimes Commission
An samar da jami'an tsaro domin bawa hukumar EFCC kariya Hoto: Economic and Financial Crimes Commission Asali: Facebook

The Nation ta wallafa cewa hukumar EFCC ta ce ta gano wasu da aka dauki nauyinsu za su gudanar da zanga-zanga kan yadda su ke bincikensu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A sauya fasalin EFCC," Masu zanga-zanga

Hadakar jami'an tsaro daga rundunar dakile aikata laifi na kar-ta-kwana a jihar Legas da jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ne su ke bawa ofishin EFCC tsaro.

Naija News ta wallafa cewa masu zanga-zanga karkashin taken a sauya fasalin EFCC na neman hukumar ta yi gyare-gyare shida a yadda ta ke gudanar da ayyukansu.

Wasu daga bukatun sun hada da neman EFCC ta rika kula da hakkin dan Adam, a daina kutsawa gidajen mutanen da ake bincike ko zargi kuma a daina lalata kayan jama'a da sunan bincike.

Sauran bukatun sun hada da bukatar hukumar ta daina daukar matasan kasar nan marasa gaskiya ne kuma jami'an EFCC su daina cin zarafin jama'a.

"Tsofaffin gwamnoni ke tunzara zanga-zanga" - EFCC

A wani labarin kun ji cewa hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta ce ta gano wadanda su ka dauki nauyin gudanar da zanga-zanga.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Dele Oyewale ya ce sun gano tsofaffin gwamnoni da wasu tsofaffin ministoci ne su ka dauki nauyin matasa su yi masu tawaye.

Asali: Legit.ng

People are also reading