An Jibge Motocin Jami'an Tsaro Domin Kare Ofishin EFCC Daga Masu Zanga Zanga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Legas- An wayi garin Juma'a da ganin tarin jami'an tsaro jibge a ofishin hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC).
An jibge jami'an tsaron a ofishin da ke titin Awolowo a Ikoyin jihar Legas saboda fargabar zanga-zangar kin jinin yadda hukumar ke gudanar da ayyukansu.
The Nation ta wallafa cewa hukumar EFCC ta ce ta gano wasu da aka dauki nauyinsu za su gudanar da zanga-zanga kan yadda su ke bincikensu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hadakar jami'an tsaro daga rundunar dakile aikata laifi na kar-ta-kwana a jihar Legas da jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ne su ke bawa ofishin EFCC tsaro.
Naija News ta wallafa cewa masu zanga-zanga karkashin taken a sauya fasalin EFCC na neman hukumar ta yi gyare-gyare shida a yadda ta ke gudanar da ayyukansu.
Wasu daga bukatun sun hada da neman EFCC ta rika kula da hakkin dan Adam, a daina kutsawa gidajen mutanen da ake bincike ko zargi kuma a daina lalata kayan jama'a da sunan bincike.
Sauran bukatun sun hada da bukatar hukumar ta daina daukar matasan kasar nan marasa gaskiya ne kuma jami'an EFCC su daina cin zarafin jama'a.
A wani labarin kun ji cewa hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta ce ta gano wadanda su ka dauki nauyin gudanar da zanga-zanga.
Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Dele Oyewale ya ce sun gano tsofaffin gwamnoni da wasu tsofaffin ministoci ne su ka dauki nauyin matasa su yi masu tawaye.
Asali: Legit.ng