Home Back

Sin Na Fatan Za A Inganta Ci Gaban Fasahar AI Cikin Lumana

leadership.ng 3 days ago
Sin Na Fatan Za A Inganta Ci Gaban Fasahar AI Cikin Lumana

Yau Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Mao Ning, ta gudanar da taron manema labarai na yau da kullum, inda game da babban taron fasahohin kwaikwayon tunanin bil adama wato AI na kasa da kasa na 2024, Mao Ning ta bayyana cewa, bangaren Sin na fatan bangarori daban daban za su tsaya tsayin daka kan ra’ayin tattaunawa tare, da ginawa tare, da raba moriya tare, kana su yi musayar ra’ayoyinsu a Shanghai, game da yadda za a inganta ci gaban fasahohin kwaikwayon tunanin bil adama cikin lumana.

Ta kara da cewa, an zartas da kudurin karfafa hadin gwiwa tsakanin sassan kasa da kasa a fannin bunkasa karfin fasahohin kwaikwayon tunanin bil adama a babban taron MDD karo na 78 ta hanyar cimma matsaya guda. Bisa wannan dama, bangaren Sin na fatan inganta mu’ammala da hadin gwiwa tsakaninsa da al’ummar kasa da kasa, da inganta aiwatar da kudurin a nan gaba.

Game da hadin gwiwar Sin da Amurka, kan batutuwan fasahohin kwaikwayon tunanin bil adama, Mao Ning ta ce, kasar Sin na son yin hadin gwiwa tare da Amurka, wajen karfafa tattaunawa da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannin, da sa kaimi ga raba moriyar da fasahohin suka kawo ga dukkanin bil’adama.

Dangane da zargin da babban sakataren kungiyar NATO ya yi, cewa kasar Sin ta kalubalanci muradun kungiyar NATO, Mao Ning ta ce, kamata ya yi kungiyar ta NATO ta yi tunani kan tushen rikicin kasar Ukraine, da kuma abin da ta yi wajen samar da zaman lafiya a Turai da ma duniya baki daya, maimakon yin watsi da alhakin dake wuyanta da wanzar da rikici.(Safiyah Ma)

People are also reading