Home Back

Hadarin mota ya hallaka bakin haure 'yan Afirka a Mexico

dw.com 2024/5/15
Mexiko Tepic | Bus-Unfall
Hoto: ULISES RUIZ/AFP

Wani hadarin mota a kudancin kasar Mexico ya yi sanadiyyar mutuwar 'yan ci-rani 3, biyu daga cikinsu 'yan asalin kasar Kamaru, yayin da wasu 5 kuma suka jikkata.

Hukumar kula da shige-da-ficen kasar bata kai ga sanar da musabbabin hadarin ba, wanda ya faru a kusa da iyakarta da Amurka, wadda ta yi kaurin suna wajen samun bakin haure masu kokarin tsallakawa cikin Amurka.

Ko a bara wasu baki haure 16 sun mutu sakamakon hadarin mota a kan wannan hanya, wadanda 'yan asalin kasashen Venezuela ne da da Haiti.

People are also reading