Home Back

Mutumin da ke fama da lalurar rashin mafarki

bbc.com 2024/7/7

Asalin hoton, Guillermo Acevedo

Guillermo Acevedo
Bayanan hoto, Likitan ɗan ƙasar Venezuela Guillermo Acevedo ya shafe tsawon rayuwarsa yana imanin cewa mafarki ba gaskiya ba ne, saboda bai taɓa yi ba
  • Marubuci, Juan Francisco Alonso
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

“Mafarki ba komai ba ne.”

Da farko, maganar ta kasance kamar wadda ba za a musanta ta ba, saboda waye bai taɓa zuwa bakin teku ba lokacin da suka sa kansu a kan gado ko kuma suka kishingiɗa a cikin motar bas don yin barci?

Za mu kuma iya samun kanmu cikin yanayi na firgita - alal misali ko mafarkin wata namun daji na bin mutum - ko kuma yanayi na ban tsoro.

Sai dai, akwai wani kashi cikin al'umma waɗanda ke mafarke-mafarke masu daɗi, inda zuciya ke hango hotuna, jin sauti har ma da wari yayin da suke barci ko kuma a zaune - ya kuma kasance abu da ba a sani ba. Dalili? Suna da zuciyar mayar da abubuwa da suka gani cikin mafarki zuwa bayyane.

Asalin hoton, Getty Images

A woman uses a computer whose screen is blank
Bayanan hoto, Acevedo ya kwatanta kwakwalwarsa da ta kwamfuta da ba ta da fuska ko kuma wadda ba za ta iya sarrafa hotuna ba

Makauniyar zuciya

Lalurar tana kuma nufin cewa kwakwalwar mutum ba za ta iya ji ko sarrafa abu ba.

Wannan shi ne yadda wani masanin lalurar kwakwalwa ɗan ƙasar Birtaniya Adam Zeman ya bayyana wannan yanayin, wanda aka fara magana a kansa a cikin shekaru ashirin da suka gabata, musamman saboda binciken da ya yi kan hotunan kwakwalwa.

“Idan aka faɗa wa yawancinmu: teburin dafa abinci ko itacen tuffa, za mu iya haifar da hoton abubuwan biyu a cikin kwakwalwarmu. Sai dai, masu fama da lalurar ba za su iya yin hakan ba,” in ji farfesan na Jami'ar Exeter ta Burtaniya.

Likita ɗan ƙasar Venezuela Guillermo Antonio Acevedo yana cikin waɗannan mutane. BBC ta tattauna da shi domin jin yadda ake rayuwa da lalurar aphantasia.

"Kwakwalwata kamar kwamfuta ce da ke da na'urar dubawa ko kuma wadda kawai za ta iya adana bayanai, amma ba ta karɓar komai," in ji shi.

Likitan ya shiga cikin mutane kashi 4 waɗanda, a cewar masana, ba za su iya hango hotunan tunani ba.

"Na yi aiki a asibitin masu taɓin hankali kuma na fara ƙarin koyo game da kwakwalwa kuma na ci karo da labarin Zeman na 2005, wanda ya yi magana game da makauniyar zuciya," in ji shi a wata tattaunawa ta wayar tarho daga garin San Sebastián na Sifaniya, inda ya rayu kuma ya yi aiki tsawon shekaru shida.

"Wannan labarin ya kwatanta yadda mutanen da ke da aphantasia suke tunani kuma waɗannan mutanen ba za su iya tunanin abubuwa ba: ba za su iya ganin hotuna a kansu ba. Sai na ce wa kaina: amma shin da gaske mutane za su iya yin hakan?".

"Abin mamaki shi ne akwai mutanen da suka ce suna iya ganin abubuwa a cikin kansu. Akwai kuma gane-gane, ba wani abu ba ne," in ji shi.

Acevedo ya shafe shekaru 31 na rayuwarsa - a yau yana da shekaru 35 - yana gaskata cewa lokacin da mutane suka gaya masa sun yi mafarki ba su ga ainihin abin da suke faɗa masa ba.

"Har sai da na gano cewa ina da lalurar rashin mafarki, na yi tunanin cewa a cikin zane-zanen barkwanci sun sanya ƙaramin girgije don mu fahimci labarin," in ji shi.

Ba kyau ba, kuma ba mara kyau ba

Asalin hoton, Guillermo Acevedo

Guillermo Acevedo making a podcast with a friend
Bayanan hoto, Duk da cewa ba ya mafarki ko kuma yin tunani kamar sauran mu, Acevedo yana ganin kansa a matsayin mai basira daɗin daɗawa ga kuma aikinsa na likita

Likitan ya ce ba wai ba ya mafarki idan ya kwanta barci ba, sai dai bai taɓa yin mafarki ba kwata-kwata. Kuma ya ce ba ya iya hango hotunan abubuwa a kansa kamar sauran mutane.

“Idan wani ya faɗa maka cewa, idan ka dubi tuffa, za ka iya rufe idonka ka kuma iya ganinsa a kanka, saboda kwakwalwarka za ta iya hango hoton, ko da ba tuffa a gabanka. Ba zan iya haka ba.

"Na san mene ne tuffa, yanayinsa da kuma kalarsa, sai dai ba na iya ganin sa a hoto idan babu shi a gabana," in ji shi. "Yanzu na gane cewa me ya sa lokacin da nake yaro aka buƙaci na zana iyalinmu, komai ya kasance cikin alkaluma, ba tare da wani bayani ba."

Shin mutumin da ba ya mafarki zai iya firgita cikin dare?

"Eh, ina fassara rashin barci mai kyau a matsayin firgita; ma'ana, daren da ba ka huta ba kuma kake jin ba ka yi barci mai kyau ba, sai dai ba na tuna ganin hotuna da suka firgita ni ba," in ji likitan.

"Na ɗauka cewa ban tuna abin da na yi mafarki a kai ba, sai dai yanzu na san cewa ba na mafarki," in ji shi.

Babu tunanin jima'i

Shin wanda bai yi mafarki ko firgita cikin dare ba zai iya yin sha'awar jima'i? A cewar Acevedo, amsar ita ce a'a.

“Ina da sandar karfi, amma ina ta gano su ta abubuwan da na gani ko na samu. Idan wani ya faɗa min wani abu da ya yi, ba zan iya hango hakan a kaina ba,” in ji shi.

Wannan shi ne dalilin da ya sa Acevedo ya ce bai taɓa fuskantar wani abu da yawanci ke nuna farkon balaga na namiji ba: yin mafarkin saduwa.

“Hakan bai taɓa faruwa da ni ba a rayuwata . Ana faɗa maku abun a makaranta da jami'a kuma koyaushe ina tsammanin camfi ce, amma ba shakka ban ce komai ba - ba na so in yi kama da wani abu mai ban mamaki," in ji shi.

Amma idan wannan bai isa ba, Acevedo ba zai iya jin muryarsa ta ciki ba; wato ba zai iya kula da zance mara sauti da kansa ba.

"Zan iya tunanin wani abu, amma ba zan iya yin magana ba saboda haka dole ne in faɗe ta. Na gano cewa gani da jin abubuwa a cikin kai zai iya zama damuwa ga mutum, "in ji shi.

Asalin hoton, Getty Images

A mask, a whip and handcuffs
Bayanan hoto, Acevedo ya yi iƙirarin cewa bai taɓa tunanin jima'i ba, sai dai bai san ko zai so ji da kuma ganin abubuwa a kansa ba

'Na ƙara fahimtar halina'

Acevedo bai yarda cewa lalurar aphantasia ya sa shi sabon abu ba. Duk da haka, ya yarda cewa tun da ya gano yana da shi, ya kara fahimtar halinsa.

"Tun da wuri na fahimci cewa abubuwan da nake so sun kasance na musamman ko wanda ba a saba gani ba, yanzu na san cewa ba bakon abu ba ne, amma bani da ikon ganin yadda wata rigar za ta kama ni, da wasu wanduna, da takalma da kuma launinsu,” inji shi.

"Idan ka ba ni zaɓi, na zaɓi abubuwan da nake so a kowane ɗayansu amma ba zan iya tunanin duka kayan ba; don haka, ina haɗa launuka daban-daban da laushi, kuma haka nake saka sutura,” in ji shi.

Ba zai taɓa yin rayuwa a matsayin mataimaki na tufafi ko kayan ado na cikin ɗaki ba.

A nasa ɓangaren, Farfesa Zeman, ya ce binciken da aka gudanar ya zuwa yanzu ya nuna cewa masu fama da lalurar rashin tunani ko mafarki ba ya shafar bsirarsu.

Batun Acevedo hujja ce, domin ba wai kawai ya yi nazarin ɗayan darussan jami'a mafi wahala ba (likitanci), amma kuma yan da tarin ilimi wanda za ku iya magana game da shi a zahiri kan kowane batu: tarihi, siyasa, tattalin arziki, kimiyya, kiɗa ko sinima. .

"Mutanen da ke fama da lalurar su kan yi aiki a fannin kimiyya da fasaha, don haka za mu iya ɗauka cewa suna da fa'ida ga abubuwan da ba za a iya gani ba," in ji masanin kan ɓangaren kwakwalwa a Birtaniya.

Acevedo ya yi imanin cewa yanayinsa ya taimaka masa a cikin aikinsa.

"Tun da yake ba zan iya tunanin abin da majinyata ke gaya mani ba, na kan yi tambayoyi da yawa don ƙoƙarin fahimtar abin da suke faɗa min kan yanayin da suke ji," in ji shi.

“Misali, majinyaci ya zo sai ya fara jin jiri. Mutane suna alakanta jiri da abubuwa da yawa wanda ba gaskiya bane. Don haka, na fara: Shin kuna jin cewa kuna da wani abu a cikin ku wanda ke haifar da matsi? Kuna jin mamaki? Kuna jin kamar abubuwa suna yawo a kusa da ku? Ina da bincike sosai,” ya kara da cewa.

The silhouette of a woman's head in profile against a smoky background

Asalin hoton, Getty Images

'Rashin tuna abubuwan da suka wuce'

Zeman ya nuna cewa ɗaya daga cikin mummunan al'amuran 'aphantasia' shi ne cewa mutanen da suke da shi ba sa iya tuna abubuwan da suka wuce ko gane fuskoki.

Shi kuwa Acevedo, ya ce idan ya shirya hutu ko cin abincin dare ya kan ji damuwa saboda rashin iya tunani ko hangen nesa. Duk da haka, don fuskantar wasu daga cikin waɗannan yanayi, ya riga ya sami fassarar ƙayyadaddun martani.

"Idan wani ya tambaye ni abin da nake so in ci, ina faɗa musu kai-tsaye: McDonald's. Tun da ina zaune a Sifaniya, inda abinci yake da muhimmanci, za su amsa: 'Ba ka da hankali ne!' kuma su ba da shawarar gidan abinci, don haka an warware matsalar,” in ji shi.

"Kuma ba don ba na son abinci ba, amma kuma ba na tuna wani abu na ƙamshi, don haka yana da wahala a gare ni in yanke shawarar abin da nake so," in ji shi.

Mece ce matsalar rayuwa a halin yanzu ba a baya ba?

"Yana da wahala a gare ni in ci gaba da dangantaka da mutanen da ba na kusa da su ba (...) Na kan yi abokantaka ta kud-da-kud a inda nake, amma idan na ƙaura ko na canza aiki dangantakar da nake da ita ta kan ɓace," in ji shi.

Asalin hoton, Getty Images

Ed Catmull sitting in front of an image of Mr Incredible
Bayanan hoto, Ed Catmull, na ɗaya daga cikin mutanen da ke fama da lalurar rashin mafarki

Abin da muka sani game da asalin lalurar

Amma mene ne ke haifar da lalurar rashin mafarki ko yin tunani? Shin cuta ce? Za a iya magance ta?

“Ba cuta ba ce, yanayin ba daidai ba ne, amma ba zan so mutane su yi imani da cewa cutar ta likita ba ce. Na gwammace in kira ta da bambanci mai ban sha'awa na ɗan adam," in ji Zeman.

Likitan kwakwalwan ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, bincike ya nuna cewa an haifi mutane da lalurar 'aphatansia', ko da yake an samu wasu lokuta da suka kamu da ita bayan bugun zuciya da raunin kwakwalwa.

"Ya zuwa yanzu, mafi kyawun bayani shi ne mutanen da ke da lalurar suna da raunin kwakwalwa a cikin wuraren da ke da buƙatar tunani," in ji shi.

"Idan kana da ikon yin tunani kuma aka ce ka yi tunani game da hasken rana, to, yaranka za su zama ƙanana, saboda ɗaliban suna mayar da martani kamar suna gaban ainihin abu. Amma hakan ba ya faruwa da mutanen da ke da lalurar rashin tunani ko hange,” in ji shi.

Game da ko wannan yanayin yana da wani magani, likitan kwakwalwan ya bayyana ƙarara cewa: “Yana da matukar wahala a haɓaka ikon gani idan ba ku taɓa samun shi ba.

People are also reading