Home Back

BAYAN SHAFE SHEKARU 10 ANA KASHE-KASHE: Majalisar Dattawa za ta kira gangamin taron ƙasa kan rikicin manoma da makiyaya

premiumtimesng.com 2024/6/26
RIKICI KAN WURIN ZAMA A MAJALISAR DATTAWA: ‘Mu tsoffin ‘yan-alewa ne, ba sabbin-yanka-rake ba’ – Sanata Goje, Ya’u

Majalisar Dattawa ta bayyana cewa za ta kira gangamin taron ƙasa, domin a samu mafita da hanyar da za a bi domin magance faɗace-faɗacen manoma da makiyaya.

Taron dai wani kwamiti ne zai shirya shi, wanda har yanzu ba a kafa kwamitin ba tukunna. Kuma za a gayyaci ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane domin kows ya je ya bayar da gudunmawar shawarwarin neman mafita.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ne ya bayyana haka, bayan da mafiya yawan sanatocin da ke zauren majalisar sun amince da hakan.

Tunanin shirya gangamin taron ya biyo bayan wata buƙata da Sanata Isah Jibrin, ɗan APC daga Jihar Kogi ya gabatar.

Jibrin ya ce rikicin baya-bayan nan tsakanin manoma da makiyaya a Jihar Kogi, cikin Ƙaramar Hukumar Omala ya ci rayuka fiye da 500, an kuma yi asarar dukiya ta miliyoyin nairori.

Ya ce a yanzu waɗanda ke da sauran kwana a gaba sun koma gidajen su, amma babu wurin zama kuma babu abinci.

Jibrin ya ce faɗace-faɗacen manoma da makiyaya ya haifar da ƙaruwar yara waɗanda ba su zuwa makaranta a Jihar Kogi.

Sanata Jibrin ya yi kira ga Majalisar Dattawa ta sa Ma’aikatar Agaji da Jinƙai da Hukumar NEMA su kai agajin gaggawa da tallafin kaya, kuma a taimake su da yadda za su ci gaba da rayuwa a mawuyacin halin da suke ciki a yanzu.

Yawancin sanatocin da suka yi magana, duk sun goyi sanatan.

Shi kuwa Sanata Titus Zam, kira ya yi a kafa dokar da za ta haramta kiwon dabbobi sakaka ana yawo, wato irin wanda Fulani makiyaya ke yi.

Ya ce dokar za ta haramta wa Fulani makiyaya yawo su na kiwo daga wannan jiha zuwa wancan.

Sanatoci da dama sun nuna goyon baya, ciki har da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan.

People are also reading