Home Back

"Zai Daƙile Rashin Tsaro": Akpabio Ya Fadi Amfanin Taken Najeriya, Ya Soki Masu Kushewa

legit.ng 2024/7/3
  • Yayin da ake cece-kuce kan sauya taken Najeriya, Godswill Akpabio ya fayyace amfanin sauya taken domin haɗin kai
  • Shugaban Majalisar Dattawa ya ce da tun farko da shi ake amfani har zuwa yanzu da ya dakile matsalar tsaro da ake fama da shi
  • Ya ce sabon taken Najeriya yana kara hadin kai da kaunar juna da kuma kishin kasa a tsakanin ƴan ƙasar baki daya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya bayyana amfanin sabon taken Najeriya.

Akpabio ya ce da tun farko ake amfani da "Nigeria We Hail Thee" da hakan ya daƙile matsalar rashin tsaro.

Akpabio ya fadi muhimmancin taken Najeriya wurin dakile matsalar tsaro
Godswill Akpabio ya ce taken Najeriya zai iya dakile matsalar tsaro a kasar. Hoto: Godswill Akpabio. Asali: Facebook

Akpabio ya fadi amfani taken Najeriya

Ya ce duka Majalisun Tarayya guda biyu sun amince da sauya taken Najeriya daga "Arise O Compatriot" zuwa "Nigeria We Hail Thee", cewar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban Majalisar ya ce sabon taken Najeriya zai kara kauna da zaman lafiya da kishin kasa da kuma hadin kai a tsakanin ƴan ƙasar, Punch ta tattaro.

"Duka wadanda ke cewa mun dawo da taken Najeriya na turawa, ya kamata su sake duba tarihin 'Nigeria We Hail Thee.'"
"Da tun farko muka dawo da taken Najeriya da zai dakile matsalar garkuwa da mutane da fashin daji da sauran rashin tsaron kasar."
"Saboda ɗan Najeriya zai rinka ganin makwabcinsa a matsayin ɗan uwa babu yadda za a yi ya cutar da shi."

- Godswill Akpabio

Akpabio ya soki masu kushe taken Najeriya

Akpabio ya ce duka masu kushe sabon taken Najeriya ba su da ilimi kan tarihin kasar da kuma dokokin kasa shiyasa suke korafi.

Ya shawarce su da su koma su sake karanta tarihi domin sanin ainihin sabon taken Najeriya da aka kawo.

Omokri ya caccaki Tinubu kan taken Najeriya

Kun ji cewa Reno Omokri ya caccaki Shugaba Bola Tinubu a karon farko bayan hawansa mulki kan taken Najeriya.

Omokri ya ce kwata-kwata ba taken Najeriya ba ne matsalar kasar a yanzu da za yi magana kan sauyawa da nufin hadin kan kasa.

Asali: Legit.ng

People are also reading